
Wani magidanci ya hannun ‘yan sanda bayan sun kamashi da laifin dirkawa ‘yarsa mai shekaru 13 ciki
Wani magidanci ya hannun 'yan sanda bayan sun kamashi da laifin dirkawa 'yarsa mai shekaru 13 ciki
Jami’an ‘yan sandan jihar Ogun sun cafke wani magidanci mai shekara talatin da tara 39 a duniya mai suna “Mfon Jeremiah”, bisa zargin dirkawa diyar sa mai shekara goma sha uku 13 a duniya ciki.
Jeremiah wanda yake zaune a rukunin gidaje na FIRRO kusa da Adesan, Mowe, a karamar hukumar Oba femi-Owode ta jihar Ogun, ya shiga hannun hukuma bayan matarsa ta kai karar sa wurin ‘yan sanda, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar “Abimbola Oyeyemi” ya bayyana batun kamun a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.
Oyeyemi yace an cafke wanda ake zargin ne bayan mahaifiyar yarinyar ta shigar da korafi a ofishin ‘yan sanda na Mowe.
Kakakin hukumar yace: Mahaifiyar yarinyar tayi korafin cewa ta gano cewa diyarta na dauke da juna biyu, sannan da ta tambayi yarinyar sai tace mata mahaifinta ne ya sadu da ita.
An kai yarinyar asibiti inda aka tabbatar da cewa tana dauke da cikin wata hudu, bayan ya karbi korafin “DPO na Mowe” SP
Folake Afen ifo ro, ya tura jami’an sa cikin
gaggawa zuwa gidan wanda ake zargi inda aka taso keyar sa.
Bayan yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ya yiwa diyar ta sa ciki, amma yayi ikirarin cewa asiri aka masa lokacin da ya aikata.
Ya gayawa ‘yan sanda cewa, ya rika mafarkin saduwa da matarsa wacce suka dade da rabuwa, kafin ya gano cewa ashe da diyar sa yake saduwa.
Oyeyemi ya kuma kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar “Lanre Bankole” ya bayar da umurnin a turo wanda ake zargin sashin hana safarar mutane da bautar da kananan yara, na hukumar domin cigaba da gudanar da bincike.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa