Advertisement
Labaran Hausa

Wani magidanci ya sheka har lashira bayan ya shanye kwalaben burkutu 11

Wani magidanci ya sheka har lashira bayan ya shanye kwalaben burkutu 11

Wani magidanci da ba a san kowanene ba wanda yayi kurin cewa zai iyashanye kwalba sha daya ta burkutu ba tare da yayi marisa ba, ya sheka lashira bayan ya kwankwade su.

Mutumin dai ya fito ne daga karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato.

Hafsat Abubakar ta kungiyar “Women Leaders of the Conflict Mediation Mitigation Regional Council” reshen jihar Filato tace:

Magidanci ya bukaci da mai siyar da burkutun ta bashi kwalba 11 sannan ya rantse cewa, zai gama da su ba tare da wani abu ya faru da shi ba.

Hafsat Abubakar wacce ta sami labarin abinda ya faru a mashayar ta gayawa jaridar Legit.ng cewa, magidancin ya samu nasarar shanye kwalba tara amma ya kasa cigaba da kwankwade sauran kwalba biyun.

Tace nan take magidancin ya mutu yayin da mai siyar da burkutun ta tattara kayanta ta ranta a na kare.

A cewar ta, kafin mutuwar magidancin ya rika aman jini ba kakkautawa ta hanci, kunne da baki.

Ta kuma kara bayyana cewa, wani mafarauci ne wanda yazo wucewa ya ga gawar mutumin sannan ya ankarar da mutanen kauyen suka binne shi, mamacin yana da matar aure daya da yaya biyar.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button