
Wani matashi dan Nageriya na shirin yin wuff da wata Baturiya wacce suka hadu a TikTok
Wani matashi dan Nageriya na shirin yin wuff da wata Baturiya wacce suka hadu a TikTok
Wani matashin dan Najeriya mai suna “Gideon Raphael” ya bayyana wa duniya baturiyar da yake soyayya da ita a shafinsa na intanet, kamar yadda “Legit.ng hausa” suka ruwaito.
Matashin dai ya shafe kusan watanni uku yana sharbar soyayyar da wannan baturiya, sannan ya saka wani bidiyo da ke nuna yadda ya tarbe ta a tashar jirgin sama a lokacin da ta iso Najeriya.
Wani matashi mai suna “Gideon Raphael” dake soyayya da wata baturiya ya yi nasarar haduwa da ita a zahiri.
Masoyan dai sun hadu ne ta kafar sada
zumunta inda Raphael din ya bayyana cewa, sun sha soyayya ne na tsawon watanni uku kafin haduwar tasu.
Sannan Raphael ya saki wani bidiyo a TikTok dake nuna yadda ya yi mata maraba a yayin da ta fito daga jirgin sama.
Masoyan, a yayin da suka ga juna a zahiri a karon farko, sun cika da farin ciki tare da rungumar juna, inda ya jefa hannunsa a wuyanta tare da yi mata jagora.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kan wannan lamarin, ga kadan daga cikin su.
Mai suna MORE_SAY IKASIAN Cewa ya yi:mata ko kaka.
Sannan Deborah Ayiku said: Yanzu ba sa bari a mazan mu su yaudare su
(matan turawa)…Aure kawai.
Shi kuwa Klimop cewa yayi: mutumina kar kayi wasa da wannan dama da
Ubangiji ya ba ka.
A cewar Richie_ralph: Wannan duk zancetn banza ne, baka san abinda ake nufi da soyayyar gaskiya ba ne. Amma
ina taya ka murna.
Ko yaya kuke kallon wannan al’amari na Wuf da ake cigaba da fuskanta daga matan Turawa, kuma me ya sa mazan mu na Najeriya ke rawar jikin auren irin wadannan Turawa?.
Rahoto daga👉 Legit.ng hausa