Advertisement
Labaran Hausa

Wani Matashi Ya Bayyana Dalilinsa Na Karshe Kishiyar Mahaifiyarsa

Wani Matashi Ya Bayyana Dalilinsa Na Karshe Kishiyar Mahaifiyarsa

Dalilin da ya sa na kashe kishiyar mahaifiya Matashi

Rundunar yan sanda a jihar Kano, ta kama wani matashi mai suna Gaddafi Sagir, bisa zargin kashe kishiyar mahaifiyarsa, da yar ta mai shekara takwas.

A wata sanarwa da kakakin yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar a Fadama Rijiyar Zaki da ke Karamar Hukumar Ungogo bayan da mahaifin matashin ya dawo ya sami matarsa, Rabi Sagir, da yar ta ta, Wacce yar riko ce, Munawwara, kwance jina-jina.

Sanarwar ta kara da cewa bayan da rundunar yan sandan jihar ta samu labarin abin da ya faru, nan take ta aika jami’anta ZUwa wajen, inda bayan an kai matar da kuma yarinyar Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad ne likita ya tabbatar da rasuwarsu

An dai kama wanda ake zargin ne a wani kango a kokari da yake na tserewa ya bar jihar.

A binciken farko da aka gudanar, wanda ake zargin ya amsa laifinsa na yin kisan inda ya ce ya yi amtani da sukun-direba wajen dabawa kishiyar babar ta sa a Wuya da kuma kai sannan ta shake yarta da dankwali har sai da ta daina numfashi.

Da ake tambayar sa dalilin aikata kisan, Gaddafi ya ce ya yi hakan ne sabo da marigayiyar ta takura wa mahaifiyarsa.

‘Har ta kai ga mahaifiya ta ta bar gidan ta koma garin mu. Ta kuma hada mahaifi na da mahaifiya ta, ta sanya ya na yi mata wulakanci iri-iri. Ni kuma hakan na bata min rai,” in ji matashin.

A cewar sa, rigima ce ta kare tsakanin sa da marigayiya Rabi da safe, lokacin da ya zo daukar abinci, inda ya kara da cewa shi ne ya dauki sukindireba ya buga mata a wuya.

Ya kara da cewa ita ma Munawwara din ya shake ta ne da kyalle zani sabo da ta “buga mun tabarya a ka. Shi ne ita ma ma shake ta.”

Ya ce shi ba ya shaye-shaye kawai dai sharrin Zuciya ne ya sanya ya aikata wannan ta’asar. Sai dai kuma ya nemi a yi masa afuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button