
Wani mummunan hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar fasinjoji 11 yayin da motar ta kone
Wani mummunan hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar fasinjoji 11 yayin da motar ta kone
Akalla fasinjoji mutum 11 ne suka kone a wani mummunan hadarin mota da ya auku a jihar Enugu, lamarin ya auku ne a daren ranar Lahadi a yankin 4-corner na kan hanyar babban titin Enugu-Port Harcourt.
Fasinjojin sun taso ne daga jihar Imno inda suke kan hanyar su ta zuwa jihar Kano, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
A wata sanarwa da kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Enugu “Daniel Ndukwe” ya fitar a ranar Litinin yace, akwai fasinjoji sha daya a cikin motar lokacin da ta kama dawuta.
Motar ta aukawa wata babbar mota ne dake tsaye a Akegbe-Ugwu akan babban titin Enugu-Port Harcourt inda ta kama da wuta wacce tayi sanadiyyar konewar mutum 11 daga cikin fasinjojin kafin a kawo musu agajin gaggawa.
A cewar sanarwar, an kai su zuwa asibiti inda likitocin dake a bakin aiki suka tabbatar da sun rasu.
Kakakin hukumar ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa, bangaren zirgar-zirgar ababen hawa na hukumar ya fara gudanar da bincike domin gano ainihin abinda ya haddasa aukuwar hadarin.
A halin da ake ciki, wasu rahotanninda ba a tabbatar da su ba, sun ce fasinjoji 14 ne suka rasu a hadarin yayin da mutum daya ake duba lafiyar sa asibiti.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa