Advertisement
Labaran Hausa

Wani mutumi ya datse mazakutarsa yace baiga amfaninta ba bayan yanke masa hukuncin daurin rai da rai

Wani mutumi ya datse mazakutarsa yace baiga amfaninta ba bayan yanke masa hukuncin daurin rai da rai

Wani mutum ya datse mazakutarsa bayan kotu ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.

Mutumin mai suna “Henry Hodges” ya yanke wannan shawarar cikin bacin rai, an yanke masa hukuncin ne bayan ya halaka wani mai gyaran waya a shekarar 1992.

Ana zargin abinda ya hassala Henry shi ne yadda ya bukaci lauyansa ya kai masa abinci na alfarma a gidan yarin amma jami’ai suka hana shi ci.

Da farko akan kisan da yayi, an yanke masa shekaru 40 ne, daga bisani kuma aka gane cewa shi ne ya halaka wani injiniya a wani otal dake Atlanta.

Lauyansa ya kai masa ziyara Cibiyar Tsaro ta Riverbend Maximum a Nashville, inda yaje masa da abincin, sai dai an hana amsa.

An ga yadda Henry yayi bayan gida ya fara shafawa a bangon cikin gidan gyaran halin, daga bisani kuma ya dauko reza a dakinsa inda ya fara yankar damtsensa a ranar 7 ga watan Oktoba.

Wani babban jami’i ya bukaci a mayarda shi daki bayan duba shi, daga nanne ya dauki reza a fasassun kwalabe inda ya guntule al’aurarsa gaba daya.

Yanzu haka jami’an sun samar da dakin da za’a kebe shi a gefe guda, sabida kada ya zama hatsari ga kansa da wasu daban, sannan kuma kada adinga daure shi tamkar dabba.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button