Labaran Hausa

Wani yaro dan shekaru 15 ya kashe mahaifiyar sa dalilin ta hana shi shaye-shaye

Wani yaro dan shekaru 15 ya kashe mahaifiyar sa dalilin ta hana shi shaye-shaye

Wani yaro dan shekara 15 dake zaune a kauyen Osubeng, gundumar Kwahu dake gabashin kasar Ghana ya kashe mahaifiyar sa sakamakon hana shi shaye-shaye da take yi.

Ance yaron mai suna lliasu Amuni ya kashe mahaifiyar tashi mai suna Sakina Amuni ne  ta hanyar buge ta da sanda sannan kuma ya yanka wuyan ta da wuka a yayin da take tsaka da aiki a gonar ta.

Wakilin majiyar mu ta Adom News
wanda ya bibiyi labarin yadda abun ya samo asali ya bayyana cewa, dama can baya yaron ya sha alwashin cewa lallai
sai ya kashe mahaifıyar tashi sabida ta
hana shi shaye-shayen tabar wiwi.

‘Yan uwan yaron dama sauran al’umma basu dauki barazanar da yaron yayi da muhimmanci ba har sai da yazo ya aikata wannan danyen aiki.

A lokacin da ‘yan sanda suka iso sun tasa keyar wanda ake tuhuma inda ‘yan sandan suka ce ya amsa laifin shi na kashe mahaifiyar tashi.

Shugaban kauyen da wannan mummunan lamarin ya faru “Nana Agyei Debrah Sasu” yace kashe mahaifiyar shida yaron yayi bai zo mishi da mamaki ba, sabili dama yaron ya taba yunkurin sanya mata guba a cikin abinci.

Nana Agyei dai ya alalakanta faruwar mummunan lamarin ga shaye-shayen miyagun kwayoyin da matasan suka dukufa akai inda yayi kira ga iyaye akan su sanya idanun akan yaransu domin kauce ma faruwar irin hakan a gaba.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button