
Wasu marasa tsoro sun sake yiwa Naziru sarkin waka wankin babban bargo bayan gargadin da yayi ‘yan Pi suna cimasa mutunci
Wasu marasa tsoro sun sake yiwa Naziru sarkin waka wankin babban bargo bayan gargadin da yayi 'yan Pi suna cimasa mutunci
Al’amarin mutane sai su kawai abarsu da Allah domin duk wani zare ido ma mutum zai yi bafa zaisa mutane su dinga tsoran saba.
Sabida Yanzu idon mutane a bude yake basa tsoran kowa sai kawai wanda Allah ya taimaka ake jin kunyarsa shine ba’a yi masa irin wa ’yan nan abubuwan da ake yiwa wanan mawakin wato Naziru Sarkin waka.
Mawakin ya fito soshiyal midiya ya jawa mutane musamman samari wanda suke hawa kan soshiyal midiya suna zaginsa kunne.
Inda yace daga yanzu sun daina dagawa kowa kafa zasu saka karar daya ga duk wanda ya kara zaginsa domin yaga abin ya fara wuce gona da iri.
Sai dai kuma bayan yayi wannan maganar ba’a wani dauki lokaci sai gashi wasu daga cikin samarin wannan garin sun kara fitowa sunyi masa wankin babban bargo.
Wanda suke nuna cewa, ko meye zai faru ya faru kasancewar shima ai yana taba wasu a cikin wannan Kafa ta sadarwa.
A wannan karan dai Naziru Sarkin waka baiji dadin wannan abinda aka kara maimaitawa a kan sa, ba domin yana ganin wannan abin da yayi ba zai sa wasu su kara yi masa fitsara ba ashe ya tsokano tsuliyar dodo sabuda yanzu ma aka fara.
Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.