
Wasu matasa ‘yan Luwadi sun kashe kansu ta hanyar fadowa daga kan gada sabida tsanar da aka musu
Wasu matasa 'yan Luwadi sun kashe kansu ta hanyar fadowa daga kan gada sabida tsanar da aka musu
Wasu matasa ‘yan luwadi su biyu sun kashe kawunan su ta hanyar fadowa daga kan wata gada mai tsayi bayan sun sumbaci junan su, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
Matasan da aka bayyana sunan su da Tigran da kuma Arsen dai sun yada wasu hotuna nasu suna sumbatar juna a shafin Instagram, tare da rubuta cewa suna murna da kawo karshen rayuwar su, kuma wannan matakin da suka dauka su biyun duka sun amince da shi.
Gama hakan keda wuya sai kawai
matasan suka sulmiyo kasa daga kan gadar Davtashen mai tsawon tako 31 wacce take a Yerevan babban birnin kasar Armeniya, kamar yadda majiyarmu ta NY Times ta wallafa.
‘Yan luwadin sun fuskanci
tsangwama daga al’umma wasu katafen cikin gida sun ruwaito cewa, matasan ‘yan luwadin na fuskantar tsangwama ne sakamakon rashin amincewar da iyayensu suka yi da alakar tasu.
Sunce Arsen ma ya gudo daga gidansu ne a dalilin hakan.
Wata hukumar kare hakkin ‘yan luwadi da sauran masu auren jinsi mai sun matasan nada sauran kwanakI masu yawa a rayuwar su, amma tsangwamar da suke fuskanta a wajen mutane ta sa
sun kashe kawunan su.
‘Yan luwadi da sauran masu auren jinsi sun saba da zaman wariya da kuma rashin jituwa da ‘yan uwan su da sauran alumma.
Wannan abu da ya faru ya kara tabbatar da cewa, rayuwar mutanen muna “LGBT” a Armeniya na cikin hadari kuma gwamnatin kasar bata damu da kare su ba, inji Pink Armeniya.
Mutane da dama sunyi mummunan tsokaci akan hotunan da wadannan matasa suka wallafa a shafin nasu na instagram.
Kasar Armeniya dai na cikin kasashen da ake kyamatar ‘yan luwadi da sauran masu auren jinsi a yankin turai.
Kasar itace ta 47 cikin kasashe 49 da suke dan mutunta hakkin masu auren jinsi a yankin.
Akalla kaso saba’in 70% na ‘yan kasarta Armeniya na ganin auren jinsi a matsayin bakon abu.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa