Advertisement
Labaran Hausa

Wata bokanya ta tada tarzoma tare da barazanar cutar da ‘yan sandan Nageriya sabida sun kama mata yaranta

Wata bokanya ta tada tarzoma tare da barazanar cutar da 'yan sandan Nageriya sabida sun kama mata yaranta

Wata bokanya mai suna Ajefunke3 a TikTok ta dauki tsatstsauran mataki bayan ‘yan sanda sun kama wasu makadanta, kamar yadda “Labarun Hausa” suka wallafa.

A wani bidiyo da ya dinga yawo, ta bayyana wata ta yi tsafe-tsafenta a wurin wani tafki yayin da ‘yan sanda suka kama mata makada.

A cewarta, bayan sun kama makadan ta tattaro makadanta inda suka afka ofishin ‘yan sanda domin su samo mutane, tace wajibi ne jami’an sugane kurensu akan mummunan aikin da suka yi mata.

Kamar yadda ta bayyana da harshen yarabanci tana cewa: Kun ganni nan a ofishin ‘yan sanda ni bokanya ce kuma ba na tsoron kowa sai Ubangiji.

Idan ban shiga hakkin kaba bana so ka shiga nawa, ‘yan sandan Najeriya sun shiga gonata kuma sai sun gane kurensu.

Yanzu haka ina ofishin ‘yan sanda ni da bokaye irina mun daura dammarar yakarsu.

Kila kunji labarin yadda aka kama Ajafunke, tabbas kafin in dawo rafi ‘yan sanda sun kama min makada na ba tare da sun yi musu komai ba.

Naje da karfin ikona na kwato su basu isa su rike min mutane na ba, sabida nasan yadda zan bullo musu ban zo da wasa ba ina da layu da sauran ababen tsafi dana tabbatar suna aiki, babu wanda ya isa yaci mutuncin Ajefunke Osiyemi.

Ko gwamnati bata isa ta ci mutuncina ba duk wanda yayi kuskuren hakan zai gane kurensa, ni Ajefunke nace hakan.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button