Labaran Hausa

Wata budurwa ta bayyana dalilin da yasa ta fasa auren saurayinta ana saura kwana 3 da auren su

Wata budurwa ta bayyana dalilin da yasa ta fasa auren saurayinta ana saura kwana 3 da auren su

Wata budurwa ta fasa auran mijin da zata aura ana saura kwana uku a daura musu aure, kamar yadda “Labarun Hausa” suka wallata.

Wata shahararriyar mai watsa labarai “Amanda Chisom” itace ta sanya hoton wallafar da budurwar tayi na cewa ta fasa auran.

A cikin rubutun da budurwar tayi a shafin Twitter tace, koda yaushe mijin da zata aura yana ce mata kudin sa na a asusun da ba a tabawa.

Duk da rokon da budurwar ta sha yi saurayin yace zai biyata duk abin data kashe a bikin, daga karshe dai ta fasa auran bayan ta samu shawara daga wajen wani masani kan lamuran aure.

A kalamanta: Wannan mutumin bai bayar da ko asi ba kuma daurin auren saura kwana uku, yana ta cewa kudin sana asusun da ba a tabawa, sannan zai biya ni daga baya.

Da take magana akan hukuncin da budurwar ta yanke Amanda Chisom” tace, Mutumin da ba ya da ko asi na sawa a baki kawai yake samu, ba ya da mota, ba gida mai kyau amma kudinsa na asusun da ba’a tabawa, ya nuna tsantsar wauta wacce za’a iya yin gadon ta.

Wasu sunyi tsokaci kan wallahar da tayi, ga kadan daga ciki.

Vivian Nwuzor ta rubuta: Eh kin yi abinda ya dace, yaje can ya karata da asusun da ba a tabawa.

Adeshola Mercy Dada ta rubuta: Eh kin yi daidai. Wannan wanda zaki auran dan 419 ne.

Nkuku-Ogechi Joy Victor ta rubuta: Kin auna arziki yaruwa, da haka ake farawa. Kafin ki ankara har kin fara biyan na cefane. Mutuminki ba yada ko sisi.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button