
Wata budurwa ta yiwa samarin data yaudara yankan kauna inda ta bude guruf a Whatsapp ta sanar dasu zata yi aure
Wata budurwa ta yiwa samarin data yaudara yankan kauna inda ta bude guruf a Whatsapp ta sanar dasu zata yi aure
Wani dan Najeriya ya bayyana yadda wata budurwar sa ta bar da bayan shirye-shiryen aurenta ya kankama, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
A cewar matashin mai suna “Prince Mudi”, budurwar ta bude guruf ne a WhatsApp inda ta sanya shi a ciki.
Sai dai a cikin kungiyar duk tsofaffin samarinta ne da yake shirin bari tayi auren ta da masoyinta.
Ya bayyana yadda ta shaida musu cewa, auren ta za tayi daga nan ta fita daga cikin kungiyar ta bar su su karasa sasanta kawunansu.
A cewar Prince Mudi, a shekarar 2017 na yi soyayya da wata yarinya na shekara daya cif.
Watarana da dare ta sanya ni a wata kungiya da ta hada a WhatsApp inda ta bayyana mana cewa, za tayi aure mako mai zuwa ta rabu da mu.
Tana gama jawabin ta tayi ficewarta don mu sasanta kawunan mu.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa