Advertisement
Labaran Hausa

Wata hamshakiyar mai kudi a garin Abuja tana neman kyakkyawan Namijin da zai mata ciki zata biya shi Miliyan uku 3M

Wata hamshakiyar mai kudi a garin Abuja tana neman kyakkyawan Namijin da zai mata ciki zata biya shi Miliyan uku 3M

Wata mazauniyar burnin tarayya Abuja dake fadi tashin zama uwa tana neman kyakkyawan mutumin da zai iya sanya wa ta dauki ciki.

Tauraruwar mai amfani da kafar sada zumunta “Uwaoma Susan Joseph” ita ce ta bayyana bukatar matar a dandalin Facebook, tare da sakaya bayanan matar, kamar yadda shafin “Hausaloaded” suka ruwaito.

Yayin da matar mai kudi ta shirya biyan duk wanda yaci sa’ar gama wannan aikin Naira Miliyan 3M, ta kuma kafa wasu sharudda yayin gudanar da lamarin.

Sannan ta bayyana cewa, matar tace duk wanda zai yi ikin za’a daure masa ido lokacin da zasu sadu, kuma zata rike shi har sai an tabbatar data samu juna biyu.

Babban dalilin da yasa za’a daure wa mutumin ido shi ne don kar nan gaba ya dawo yana nemanta don dansa.

Sannan tace, Suzy dan Allah ki rubutu game da ni, ina bukatar mutumin da zai mun ciki kyakkyawan mutum, za’a daure masa fuska duk lokacin da zai kwanta dani kuma zan biya shi.

Abinda yasa za’a rufe masa fuska shi ne don kar ya dawo nan gaba yana neman a dan, zan riken shi har sai an tabbatar na samu ciki sannan zai tafi.

Ina zaune a Abuja ni zan kula da komai na kudi dan Allah ki boye sunana, tace kudin da zata biya miliyan uku cas 3M.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kan wannan lamarin.

Melodiesofpraise tace: Lallai kuwa, Allah yasa kar gobe ya dawo yaje fa ki cikin matsala, ya matsa miki sai kin nuna masa dansa, shawara ki bar matar ta nemi wanda zai mata aiki da kanta.

Queen Isaac Emejuru tace:

Ki rufe idon dan wasu har sai kin dauki ciki ya kenan idan ke ba mai dauka da wuri bace? Zaki cigaba da rufe masa ido har tsawon shekara biyu kenan? Ya za’ai idan baki samu cikin ba, shin zaki biya ladan gwaji?.

Rahoto daga👉 Hausaloaded

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button