Advertisement
Labaran Hausa

Wata kyakyawar Budurwa zata yi wuff da Direban Bolt wanda ta fara turawa sako a Whatsapp

Wata kyakyawar Budurwa zata yi wuff da Direban Bolt wanda ta fara turawa sako a Whatsapp

Kyawawan hotunan kafin aure na wata Budurwa ‘yar Najeriya da direban motar haya ta bolt sun karade shafukan sada zumunta.

Budurwar wacce zata zama Amarya mai suna “Omolayoeni” ta dai shiga motar direban bolt din shekara biyu da suka gabata, kamar yadda “Labarun Hausa” suka wallafa.

A lokacin da suke tafiya sai taga direban yana da kyau sosai, don haka sai ta tura masa Sako ta WhatsApp bayan nan inda ta bukaci da ya ajiye lambar wayar ta.

Direban mai suna Akinsola ya yarda ya ajiye lambar wayar ta, shekara biyu tun bayan haduwar su soyayyar su tayi karfi har sun shirya yin aure yanzu.

An saka hoton yadda hirar su ta farko ta wakana a Twitter inda aka rubuta: To dai, shekara biyu da suka wuce kanwata ta kira bolt inda taga kyakkyawan saurayi,  ta kasa jurewa dai har sai data tuntube shi.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su akan wannan lamarin.

Olayemi Yemaji ya rubuta cewa: Da ace direban bolt din ne yayi haka, da ance yayi cin zarafi, amma tun daba haka bane sai mubi sahu ayi ta cewa Awwn.

Olamilekan ya rubuta cewa: Irin ‘yan matan da suka ki ba direbobin fuska suyi hira da su, za kagan su anan suna cewa Awwn da Ubangiji yaushe’ Walahi enigbadun.

Justin Kaycee ya rubuta:”Don Allah ta ya mutum zai yi rajistaya zama direban bolt ko Uber? Inatunanin na bolt ya fi.”

ICyril Michael ya rubuta cewa: Ina son irin wadannan matan, suna neman abinda suke so ko da ba suyi nasara ba zasu amince da hakan, kusani cewa ba wata cutuwa a jaraba sa’a, Maza masu karamin tunani ne kawai zasu ce ta kosa ne.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button