Advertisement
Labaran Hausa

Wata Mata ta shigar karar da uban ‘yayanta kotu bisa zargin ya yi mata fyade

Wata Mata ta shigar karar da uban 'yayanta kotu bisa zargin ya yi mata fyade

Wata mata mai yara biyu ta maka mijin da zata aura kotu bisa zargin yayi mata fyade.

Matar ta maka mijin da zata aura a wata kotu dake Yola babban birnin jihar Adamawa.

Matar wacce ta haifi yara biyu da wanda zata aura din sannan ta kwashe shekaru suna rayuwa tare, na zargin shi da laifin yayi mata fyade shekara goma da suka gabata, kamar yadda “Labarun Hausa” suka wallafa.

A takardar karar mai lamba UAC4/CA/322/2022/ wacce aka shigar a ranar Jumaa 28 ga watan Oktoba, matar wacce take rayuwa tare da wanda zata aura a hanyar barikin sojoji a Jimeta Yola, tace yayi mata fyade shekara goma da suka gabata lokacin da ta kawo masa abinci bayan ya bukaci da tayi hakan.

Tayi zargi a cikin karar cewa, bayan mun fara soyayya ya kira ni a waya yace na dafa masa abinci na kawo masa sabida baya da lafiya.

Yayi amfani da wannan damar yayi min fyade, bayan ta kawo masa abincin tayi ikirarin cewa ya sadu da ita ba tare da amincewar ta ba.

Bayan hakan ya auku ta samu juna biyu, lokacin da ta gaya masa tana da juna biyu sai yace sam ba na shi bane.

Bayan ta haihu ya yarda cewa jaririn na shi ne sannan ya nemi data yafe masa, daga nan sai suka fara rayuwa tare inda ta kara samun wani juna biyun bayan wasu shekaru sannan ta haifi yaro na biyu.

Tayi ta yunkurin ganin yaje ya gana da yayenta domin suyi aure amma sai yaki zuwa kwata-kwata.

A dalilin sa na kin yarda suyi aure da kuma rashin bata cikakkiyar kulawa
ita da yaranta, matar ta maka shi agaban kotu kan zargin laifuka uku.

Ta zarge shi da yi mata fyade, duk da an tada yi mata barazana, ta kuma zarge shi da nuna halin ko in kula wajen kulawa da ita da yaran su guda biyu.

Ana zargin cewa, ta shigar da karar ne bayan ta fahimci cewa yana shirin korar ta daga gidan sa domin ya auro wata.

Mijin da zata aura din dai ya musanta dukkanin zarge-zargen da take masa, mai shari’a Ibrahim Musa Ulenda, ya daga sauraron karar har sai ranar 1 gawatan Disamba, 2022.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button