Advertisement
Magunguna

Ya kamata kusan wasu abubuwa guda 6 wadanda suke hana Miji da Mata jin dadin jima’i yayin saduwa domin ku magance su

Ya kamata kusan wasu abubuwa guda 6 wadanda suke hana Miji da Mata jin dadin jima'i yayin saduwa domin ku magance su

(1) Rashin ingancaccan abinci mai lafiya.

Idan mace bata cin abinci mai kyau ta koshi wanda zai inganta lafiyarta da jikinta da sinadarai na ni’ima, to sha’awarta tamkar shukace wacce bata samun ruwa wacce zata mutu.

Kifi, naman kaza, madara, yogot, hanta, kwai, zuma, dabino, aya, gyada, kankana, ayaba da sauran abincin mai gina jiki da kuzari tare da ‘yayan itatuwa zasu iya cika mace da sha’awa da ni’ima bayan daukewar sha’awa.

Wadannan abubuwa marmari da abinci tamkar taki ne da ruwa ga shuka, wato sha’awar ‘yar mace, don haka mazaje su siyama matansu kayan dadi domin moruwa dai-dai gwargwadon hali.

(2) Saurin inzalin maigida, rashin karfin mazakuta.

Wannan matsalar nada alaka da mazajen aure kai tsaye, wannan matsalar na cutarwa mata sosai kuma wani lokacin tana da alaka kai tsaye da rashin karfin mazakuta.

Idan akwai karfin mazakuta ga namiji koda ba babba bane azzakarin zai iya gamsar da iyalinsa idan akwai karfi sosai, kuma zai dade yana saduwa da iyalinsa har ta biya bukatarta.

Haka kuma idan muka kalli matsalar ta wata mahangar, hakan na faruwa ne sabida rashin sha’awar namiji wato sinadaran jima’insa (sex hormones /low testosterone) sun ragu ko sunyi kasa ko kuma hawan jini ko ciwon suga suke haddasa masa matsalar koma yawan sinadarin kolesterol ko wasu matsalolin zagayawar jini.

Don haka cin abinci mai inganta lafiya da harkar jima’i ko magani mai kyau da likita yayi izini dashi zai iya gyara matsalar.

Mafi yawan lokuta mata na bukatar tsawon lokaci kamin su kawo sabanin lokacinda maza da dama ke iya jurewa su biya musu bukata.

Don haka yin wasanni yima iyali wasa tsawon lokaci na iya fansar lokacinda maigida baya iya kaiwa ta yanda mace zata iya fara biyan bukatarta ko kawowa kamin saduwa da ita.

(3) Rashin fashimtar yanayin Mace da bukatunta na kwanciya.

Ko wace mace da irin bukatunta na jima’i akwai irin abinda take so ayi mata da nau’in kwanciyar da take jin dadinta amma da yawa kunya na hana mata bayyana abinda suke so, don haka sai subar mazajensu cikin duhu suna ta kokarin jarraba abubuwanda basa yi musu.

Don haka matan aure su fidda kunya domin tattaunawa da mazajensu akan abinda suke so wajen jima’i da mazajen suma su bayyana irin bukatun nasu domin fahimtar juna da jin dadin rayuwar aurensu.

Haka kuma yana da kyau maigida ya rinka lura da nazari akan bukatun wasu sassan jikin matarsa idan mai yawan kunya ce.

Yau da gobe zai iya gane abinda ke yimata wajen saduwa, yau da gobe zaka tara ilimi mai yawa akan bukatar matarka amma idan har kana lura da kyau.

(4) Wasa da gaba.

Idan mace na wasa da farjinta wato (istimna’i) da yatsa ko wani abu take sakawa zai iya sanyawa taji bata jin dadin jima’i ko gamsuwa da maigidanta sai tayi istimna’i, sabida tafi kowa sanin jikinta da mallakarsa ta gano bukatunta na shaidan wanda aurenta bazai iya biya mata ba.

Musamman bainar zawarawa da ‘yan mata wannan abune game gari, da yawa sun saba biyama kansu bukata kuma zai iya shafar tarayyarsu da mazajen da zasu aura nan gaba.

Kamar dai yanda muka yi bayani a wata wallafar mu a can baya cewa, istimna’i nasa wuyar kawowa ga mace wajen jima’i dalilin koyama jikinta da sai an taba wani sashen farji don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne azzakari baya taba wurin lokacin saduwa a zahirin jima’i.

Don haka istimna’i yana sa rashin gamsuwar jima’i ga mace, mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita.

Jikinta ya riga ya koya tayima kanta horo zata rinka tunanin mijinta baya iya gamsar da ita ko mazajen data aura, sabida sabon da tayi da koyama jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima’i a cikin sunnar aure ta canza dabi’ar ta.

Da yawa zaka samu cewa mata masu yawan istimna’i basu jin dadin jima’i sai istimna’i, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna’i a bandaki bayan saduwa da mazajen aurensu, wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure.

(5) Aljanin soyayya (Jinnul aashik.

kamar dai yanda muka tattaro wasu bayanai daga Zauren Fiqh da wata mabubbugar, Aljani na iya shiga jikin mace da sunan soyayya ya dinga saduwa da ita koma ya aureta.

Hakan zaisa Aljanin ya hana ta aure, ko haihuwa, ko rashin zama lafiya da miji idan tayi auren, kuma zaisa mata daukewar sha’awa da ni’ima ga mijinta, ko zubar jini ko ruwa mai wari koma gaban mijin yaki mikewa lokacin saduwa.

Zata rinka mafarkin ana saduwa ta ita wanda shedanin zai zo mata da siffar mijinta ko wani mutum, ko siffar mace na saduwa da ita, ko ta dinga ganin mutum tsirara a gabanta.

Wadannan suna daga cikin alamomin, kuma dalilin take hana mace jin dadin jima’i ko sha’awa.

(6) Rashin sha’awa sabida karancin sinadarin jima’i a jiki ko ciwon damuwa.

Karancin sinadarin jima’i da sauye-sauyen halittar mace( low estrogen) na iya haddasa sallacewar sha’awar mace.

Alamomin karancin sinadarin sune: jin zafi wajen jima’i sabida rashin ruwan gaban mace, zuwan al’ada ba akan lokaci ba ko rashin yinta, karuwar cututtukan mafitsara, canjin yanayin rai daga farin ciki zuwa damuwa, ciwon nono, ciwon kai, ciwon damuwa, kasala, wuyar lura ko nazari, rashin kwarin kashi, da sauransu.

Idan ba’a magance matsalar ba zai iya sanya mace rashin haifuwa.

Abubuwanda ke haddasa karancin sinadarin sun hada da: ciwon koda mai tsanani, tsananin motsa jiki, zufar dare, gumin jiki, rashin bacci, rashin cin abinci sabida tsoron yin kiba.

Haka kuma ga mata wanda suka haura shekara 40 na haihuwa karancin sinadarin na iya zama alama ne cewa sun kusa gama al’ada.

Allah yass mudace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button