
Yadda Aka Cafke ‘Yar Aiki Na Kokarin Sanya Guba A Ruwan Shan Matar Gida
Yadda Aka Cafke 'Yar Aiki Na Kokarin Sanya Guba A Ruwan Shan Matar Gida
Asirin wata ‘yar aiki ya tonu yayin da aka kamata tana kokarin sanya maganin kwari a ruwan shan uwargidanta.
A wani bidiyo da nan da nan ya karade shafukan sada zumunta, an ga ‘yar aikin ta durkusa kan guiwoyinta tana amsa tambayoyin uwargidan na ta bayan an yi ram da ita.
Kamar yadda muka samo daga shafin Bestshowbiz.
Yar aikin gidan ta bayyana cewa tayi alkawarin sai ta halaka duk wanda ya gaya mata wata maganar da ba tayi mata dadi ba a rai.
A cewar ta, ta cire ‘yan makullan dakin matar gidan daga wurim da aka saba ajiye su, ta shiga dakin sannan ta sanya gubar a cikin ruwan shan ta.
Sai dai tayi rashin sa’a domin duk wannan tuggun da take shiryawa an dauka a kyamara yayin da take aikatawa.
Wannan lamarin dai ya sanya mutane da dama tunanin ko wane irin abu matar gidan take yiwa yar aikin da har ya sanya tayi tunanin ta cutar da ita, yayin da wasu kuma Sun goyi bayan matar gidan inda suka bukace ta da ta gaggauta korarta daga gidan.
Wasu daga cikin ‘yan Najeriya na goyon bayan matar gidan inda suka
bata shawarar da ta koreta daga gidan ba tare da bata lokaci ba.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.