
Yadda Aka Ceto Ran Wani Mutum Da Yayi Shekaru Ashrin A Kule A Wani Daki A Jihar Kaduna
Yadda Aka Ceto Ran Wani Mutum Da Yayi Shekaru Ashrin A Kule A Wani Daki A Jihar Kaduna
Yanzunan majiyarmu ta samu labarin yadda yan sanda suka ceto ran wani mutum da yayi shekaru ashrin a kule a wani daki kamar yadda shafin Bbc Hausa suka rawaito
‘Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ƙaddamar da bincike kan dalilan da suka sanya aka kulle wani mutum a cikin ɗaki na tsawon shekara 20
A ranar Laraba ne ƴansandan suka ceto mutumin mai suna Ibrahim Ado, mai kimanin shekara 67 a wani yanki na birnin Kaduna da ake kira Bayajida
Mai magana da yawun rundunar ƴansanda a jihar Kaduna ASP Muhammed Jalige, ya ce jami’an rundunar sun kai samame a gidan da aka kulle mutumin ne bayan samun bayanan sirri
Ya ce mutumin mai kimanin shekara 67 ya kwashe tsawon shekarun ne yana garƙame a ɗakin, inda a nan yake cin abinci da kuma duk lamurransa.,, kuma an same shi cikin mummunan yanayi
Yanzu haka dai mutumin na samun kulawa a asibiti’
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.