
Yadda aka kama wani magidanci yana kokarin sayar da ‘yar cikin sa kan kudade Naira Miliyan Ashirin 20M
Yadda aka kama wani magidanci yana kokarin sayar da 'yar cikin sa kan kudade Naira Miliyan Ashirin 20M
Wata babbar kotun yanki a Makurdin jihar Binuwai ta bayar da umarnin tsare wani mutumi wanda aka gurfanar a gabanta a bisa kokarin sayarda ‘yar cikinsa kan Naira miliyan 20, kamar yadda shafin “Hausaloaded” suka ruwaito.
‘Yan sanda ne suka gurfanar da mutumin da abokinsa bisa zarginsu da laifukan hadin baki domin aikata laifi da satar mutum da kuma safarar mutane.
‘Yar sanda mai gabatar da kara “Veronica Shaage” ta sanar da kotun cewa, an kama wadanda ake zargin ne a kokarin su na sayar da wata yarinya mai shekaru hudu kan kudade Naira miliyan ashirin.
A lokacin da suke tsaka da kulla cinikin ne da wani mai suna Terna, ‘yan sanda suka far musu inda wadanda ake zargin suka shiga hannu shikuma Terna ya cika wandonsa da iska.
Veronica ta karanto sassa daban-daban na dokokin fenal kod na jihar da masu laifin suka karya, ta kuma roki kotun da ta zartar musu da hukuncin da ya dace.
Alkalin Kotun “Dooshima lkpambese” tayi watsida ikirarin masu karar na hurumin kotun na sauraron shari’ar.
Sannan ta aika dasu gidan gyaran hali domin a cigaba da tsare su har zuwa ranar daya ga watan Disamba a matsayin ranar da za’a cigaba da sauraron kara.
(NAN) Wata kotu a Makurdi jihar Binuwai ta bada umarnin tsare wani magidanci mai shekaru 45, a bisa zargin sayar da ‘yarsa mai shekaru hudu kan kudade Naira miliyan ashirin.
‘Yan Sanda sun kamo mahaifin yarinyar ne tareda abokinsa bisa zarginsu da aikata laifin hadin baki da sata da safarar karamar yarinya.
Alkalin kotun dai ta bada umarnin tsare su a gidan kaso na Makurdin, tare da dage sauraren karar zuwa ranar 1 ga watan Disamba.
Tun da farko ‘yar Sanda mai gabatar da kara “Insfekta Veronica Shaagee” tace, sakamakon rahoton sirri da suka samu ne suka kamo mutanen aka tsare su a sashen binciken manyan laifuka dake Makurdi.
An dai kama magidancin da abokinsa ne suna tsaka da cinikin yarinar, sai dai wanda ake zargin zai saye ta ya cika wandonsa da iska.
Laifin da Shaagee tace, ya sabawa sashe na 97 na kundin Penal Code na jihar Binuwai na 2004, da sashe na 3(2) na dokar hana satar dan Adam na 2017, da na 2006 19 (1).
Rahoto daga👉 Hausaloaded