Advertisement
Labaran Hausa

Yadda aka yi nasarar gano wata karamar yarinya mai shekaru uku a cikin rijiya bayan ta baya tsaron kwanaki uku

Yadda aka yi nasarar gano wata karamar yarinya mai shekaru uku a cikin rijiya bayan ta baya tsaron kwanaki uku

An tsinci wata karamar yarinya “Lydia Azatyom” mai shekara uku a duniya a cikin wata tsohuwar rijiya, kwanaki uku bayan tayi batan dabo a unguwar Tudun Wada ta Jos, babban birnin jihar Filato.

Ganin karshe da aka yiwa karamar yarinya ya auku ne a ranar Alhamis 27 ga watan Oktoba, tana wasa da kawayenta a kofar gidan su kafin bacewar ta, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.

Duk wani kokarin iyayenta da makwabta na ganin an gano inda take yaci tura, har sai zuwa bayan kwana uku, lokacin da wani Dauda Dung ya tabbatar da cewa an gano ta.

Shafin LIB ya ambato cewa, wani matashi ne ya gano yarinyar a cikin wata tsohuwar rijiya a wani kango dake unguwar.

An tattaro cewa, matashin yaje kangonne domin yin bayan gida inda yaji karar alamun motsi a cikin rjiyar wacce bata da ruwa.

Ginin kangon dai an dade ba’a amfani da shi inda yanzu aka mayar da shi wurin zubar da shara da yin bahaya.

Lydia ta samu raunika a wajen kanta inda aka garzaya da ita asibiti inda take cigaba da samun kulawar da ta dace.

Har yanzu dai ba’a da masaniyar cewa ko yarinyar bisa tsautsayi ta fada cikin rijiyar ba ko kuma wani ne ya jefata ciki.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button