Advertisement
Labaran Hausa

Yadda Dr Na’ima Idris take wayar da kan al’umma kan tsaftace muhalli

Yadda Dr Na'ima Idris take wayar da kan al'umma kan tsaftace muhalli

Kamar yadda zaku gani a cikin hotunan dake kasa yanzu haka Dr. Naima ldris Usman ta fadada ayyukanta na sa kai, inda take kokarin wayar da kan alumma muhimmancin kula da tsaftar muhalli.

Da kuma hanyoyin da ya kamata subi domin bawa kansu kariya daga kamuwa da cututtuka ko samin raunuka a wajejen zubar da shara ko yawon neman kayan jari bola da yara da matasa ke yi domin neman nakai

Dr. Naima ldris Usman wacce ake yi wa
lakabi da (Girls Talk Series), matashiyar Likita ce wacce tayi suna wajen bawa al’ummna shawarwari kan harkokin kiwon lafiya musamman a sabbin kafafen sadarwa nazamani, inda dumbin al’umma ke amfana da iliminta wanda ta ke bayar da shi kyauta.

Dr. Naima ldris Usman wacce ake yi wa
lakabi da “Girls Talk Series” matashiyar Likita ce wacce ta yi suna wajen bawa aľ’umma shawarwari kan harkokin kiwon lafiya, musamman a sabbin kafafen sadarwa nazamani “Social Medi”.

Inda dumbin al’umma ke amfana da iliminta wanda ta ke bayar da shi kyauta.

Cikin hotunan Dr. Naima ldris sanye take da safar hannu da takalmin kafa akan wannan bola da ake zubar da shara, inda take nunawa al’umma musamman ma yara dake zubar da shara da ‘yan jari bola cewa.

Ba haka kawai ake hawa bola garangatsau ba, ya kamata ana saka kayan kariya daga samun rauni ko kamuwa da cututtuka.

Rahoto daga👉 Hausaloaded

Ga hotunan a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button