Labaran Hausa

Yadda jaruman kannywood suka yi dandazo wajan gudanar da bikin bude katafaren shagon saida tufafi na Abubakar Maishadda

Yadda jaruman kannywood suka yi dandazo wajan gudanar da bikin bude katafaren shagon saida tufafi na Abubakar Maishadda

Kamar yadda kuka sani dai furodusan masana’antar kannywood “Abubakar Bashir Maishadda”, ya bude wani katafaren shagon saida tufafi mai suna ” TexTile”.

Abokan sana’ar sa jaruman kannywood da mawaka sun halarci wajan taron bikin bude shagon nasa, inda suke nuna murna da tayi shi farin cikin bude wannan katafaren shagon.

Abubakar Maishadda yayi wani dan gajeren bayani a shafin sa na sada zumunta instagram, a lokacin da ya wallafa wani hoto da yake nuna cewa ya bude wannan shagon nasa.

Inda ya fara da cewa: Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin kai. Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.).

Ni ABUBAKAR BASHIR MAISHADDA Ina Farin cikin Gayyatar Dukkanin Masoyana da suke Fadin Nigeria, Dama Abokanan Sana’ata Zuwa Wajen Bude Shagona “maishadda_textile.

Na Sai da Yadika, Shaddodi, Huluna, Jakunkuna, Takalma, Dogayen Riguna da sauransu, Ranar 30 ga watan September Inn shaa Allah.

Bayan wannan jawabi da Abubakar Maishadda yayi na, sai kuma ya sake wallafa wasu hotunan abokanan sana’ar sa na kannywood a lokacin bude shagon nasa.

Ga hotunan a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button