Advertisement
Labaran Hausa

Yadda Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Fashe Da Kukan Tare Da Neman Mijin Aure

Yadda Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Fashe Da Kukan Tare Da Neman Mijin Aure

Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai suna Princess Mimi ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta koka kan cewa har yanzu bata auru ba duk da yawan shekarunta.

Matashiyar mai shekaru 38 ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda ta dungi sharban kuka a cikin wata mota yayin da take fallasa asirin zuciyarta.

Princess ta ce zata cika shekaru 39 a bana, kuma har yanzu bata yi aure ko mallakar da nata na kanta ba kuma bata da wani tsayayye da zai fito neman aurenta.

Ta bayyana lamarinta a matsayin mara tabassa sannan ta roki Ubangiji da ya kawo mata agaji

Ba aure. Ba da. Babu wani tsayyen namiji. Bani da tabbass. Ya Allah ka taimake ni,” ta rubuta a jikin bidiyonta. A daidai lokacin wannan rubutun, fiye da mutum 704k ne suka kalli bidiyon yayin da jama’a suka karfafa mata gwiwa.

Kalli Wallafarta a kasa

Pwincex Mimi

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun Kalli wannan bidiyan zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button