
Yadda Mai Sayar Da Pure Water Ya Durkusa Kasa Yana Godiya Ga Allah Bayan Diyarsa Ta Kammala Jami’a
Yadda Mai Sayar Da Pure Water Ya Durkusa Kasa Yana Godiya Ga Allah Bayan Diyarsa Ta Kammala Jami'a
Wata mata ta yi murnar Kammala jami’a tare da iyayenta da ‘yan uwanta kamar yadda ta bayyana wa duniya, Legit.ng ta ruwaito.
A bidiyon an ga inda ta tafi da gudu ta shiga shagon siyar da ruwan leda inda mahaifinta ke sana’arsa ta rungumi shi.
Mahaifin nata cike da farinciki ya durkusa da guíwoyi kasa yayin da yake godiya ga Ubangiji akan niimar da yayi masa ta kammala karatu da diyarsa tayi.
A bidiyon wanda ya bazu a kafar TikTok, bayan yayanta ya sanya mata hannu ne tayi gudu zuwa shagon mahaifinta.
An ga inda mahaitin nata ke wakoki na murna har ya kai ga durkusawa kasa don yi wa Ubangiji godiya.
A bidiyon, yarinyar ta bayyana cewa da sana’ar fiyo wota iyayenta Su ka dauki nauyin karatunta har ta gama.
An ga inda mahaifiyarta ke muma inda aka ga wata yarinya tana siyar wa kwastomomi ruwan, ta yuwu kanwarta ce.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.