Advertisement
Labaran Hausa

Yadda malamin makarantar mu da nake dauka a matsayin uba yayi yunkurin yin lalata da ni, cewar wata Daliba

Yadda malamin makarantar mu da nake dauka a matsayin uba yayi yunkurin yin lalata da ni, cewar wata Daliba

Wata daliba ta bayyana yadda malaminta data dauka kamar uba yayi yunkurin yin lalata da ita, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.

Lamarin dai ya auku da ita ne a shekararta ta farko da shiga jami’a, dalibar ta ce ita sabanin irin dalibannan ne marasa kokari wanda ke bayar da kansu don samun cin jarabawa ga malamai, kokarin ta ne yasa har malamin nasu ya santa yayi kokarin yin lalata da ita.

Da farko malamin ya fara nuna mata kulawa akan karatunta inda ya rika bata shawarwari kan yadda zata kara mayar da hankali akan karatun nata, kafin daga bisani ya bayyana hakikanin abinda ke ran sa.

Malamin ya kuma gaya mata cewa, duk lokacin da take da matsala ta tuntube shi, bayan kwana biyu da yin wannan zancen nasu ya kirata a waya inda ya bukaci da ta same shi a ofis.

Ta bayyana cewa, bayan ta shiga makaranta taje ofis din malamin domin jin dadin kiran da yayi mata.

Bayan mun gaisa cike da mamaki sai na ga ya tashi ya tafi kofa ya rufe sai na tsaya dai in ji me zai ce.

Bayan ya rufe kofar abin da ban taba
tunani ba a wannan lokacin shi ya faru, shi ne na ga mutumin ya fara tahowa inda nake kafin nayi magana nace ma wani abu har ya rike hannuna, nake ce masa meye haka?.

Yace min ai ba komai me ya sa nake abu
kamar yarinya ne bayan na shiga jami’a,
yace ai ni babbar yarinya ce yanzu tun da
na shiga jami’a, sai na ce ni ba babbar
yarinya bace kuma ni ba abin da iyayena
suka turo ni na yi ba kenan, kafin na ankara ma ya fara shafa min fuska.

Dalibar tace, daga karshe dai sai data kai malamin ya fito fili ya gaya mata abin da yake so ya yi da ita, inda daga nan ta fara kuka tana karkarwa.

Tayi masa barazanar cewa zata yi masa ihu idan bai kyaleta ba, hakan ya sanya ya kyaleta tare da yi mata barazanar cewa zata gani akwaryarta.

Dalibar tace, tun daga wannan lokacin ta fara ganin sakamakon ta na jarrabawa na raguwa a makarantar.

Daga karshe bayan malamin ya cigaba da kiranta yana mata tayin ta amshi bukatar sa ta yanke shawarar sauya makaranta.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button