
Yadda Matashi Dan Shekaru Yayi Garkuwa Da Kansa Ya Karbi N1m Kudin Fansa Daga Wajen Mahafinsa
Yadda Matashi Dan Shekaru Yayi Garkuwa Da Kansa Ya Karbi N1m Kudin Fansa Daga Wajen Mahafinsa
Yan sanda sun kama wani matashi mai shekara 19 a Jihar Adamawa, Isreal Emmanuel saboda shirya garkuwa da kansa tare da karbar Naira millyan1na tansa daga mahaifinsa.
An tattaro cewa a ranar Asabar ne Emmanuel da wasu abokansa uku suka shirya garkuwar karya suka yi magana da mahaifinsa don karbar fansa, The Nation ta rahoto.
Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da kama Emmanuel wanda ya amsa cewa shi ya shirya garkuwa da kansa tare da abokansa biyu, Fartaci Mustapha da Zakka Nuhu, dukkansu daga karamar hukumar Mubi ta Arewa
Yan sandan na kan neman mutum na uku da ake zargi mai suna Abdulhamid Mohammed.
Emmanuel, mazaunin Mararraba Mubi, ya hadu da Zakka Nuhu a yankin Welcome to Mubi na garin Mubi, ya tafi Muvir a karamar hukumar Mubi ta Arewa ya boye kansa a gidan Fartaci Mustapha na kwana shida yayin da suke tattauna batun kudin fansar daga mahaifinsa.
Fartaci Mustapha ya kira mahaifin Isreal a waya, ya fada masa game da ‘sace’ dansa.
Bayan Fartaci ya gabatar da kansa ga
Emmanuel a matsayin daya daga cikin masu garkuwar, ya mika waya ga lsreal kuma suka yi magana.
isreal ya tada wa mahaifinsa cewa an sace ni kuma ana bukatar biyan kudin fansa kafin a sako shi.
Bayan kwana shida a Muvir, Isreal ya dawo gida Mubi ya hadu da sauran abokansa da suka hada baki suka matsa wa mahaifinsa har sai da ya
biya Naira miliyan 1.
Ya umurci Fartaci da Abdulhamid su tafi daji a Mararaba Mubi don karbar fansar.
Mutane biyun sun hadu da Emmanuel amma Abdulhamid ne ya karbi kudin a inda aka ajiye musu.
Abin takaici ga sauran wadanda suka shirya garkuwar, Abdulrasheed ya ce N500,000 kacal nahaifin lsreal ya biya matsayin fansa.
Isreal ya koma gida da N200,000 a matsayin kasonsa ikin N500,000 din, kuma tunda ya san ya yaudari abokansa sai ya tsere kafin, yan sanda su san da batun.
An kama sauran wadanda aka zargin bayan mahaifin lsreal ya kai korafi ofishin yan sanda, duk da cewa a lokacin bai san dansa ne ya yi garkuwa da kansa ba.
Kakakin yan sandan Adamawa, SP Suleiman Nguroje, wanda ya tabbatar da kamen ya bada tabbacin cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.