
Yadda mawaki Rarara yaci mutuncin wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar Kano a sabuwar wakarsa
Yadda mawaki Rarara yaci mutuncin wasu daga cikin manyan 'yan siyasar Kano a sabuwar wakarsa
Wata sabuwar wakar Rarara mai taken lema ta sha kwaya da mawakin ya dora a shafin sa na facebook ta janyo cece-kuce, kamar yadda “Labarun Hausa” suka wallafa.
Fasihin mawaki Dauda Adamu Abdullahi Kahuta wanda aka fi sani da Rarara kamar dai yadda ya saba, ya saki wani dan gutsire na daga cikin sabuwar wakar tashi wacce yayi wa dan takarar shugabancin kasa na APC “Bola Ahmed Tinubu”.
A cikin wakar an jiyo shi yana habaici ga wani da bai ambaci sunan shi ba wanda mutane da dama suke ta hasashen ko da wa Rarara yake a cikin wakar.
Ga dai kadan daga cikin baitocin nasa.
(1) – Kace acire sunana wannan naji
(2) – Dama bance a sakani ba inda kaji
(3) – Duk wani taro da kake kaina to naji
(4) – Mu harkar Tinubu ba saida takarda ba
(5) – Shi dai zabo a sanina baya chara
(6) – Ko a buga ko abari dai Nine Rarara
(7) – Na ari rigar gamji ko dan nai sara
(8) – In dutse yakafu badai turewa ba
Sai dai tun bayan sakin wannan dan guntun bangare na wakar a Facebook, mutane da dama suna ta tofa albarkacin bakinsu kan yadda suka fahimci wakar.
Wasu sun alakanta wakar Rararan da wasu manyan masu mukamai a jihar Kano.
Shahararriyar ‘yar soshiya media “Hauwa Faruk” ta wallafa a shafin ta cewa, tana kira ga ‘yan siyasa da su guji alaka da Rarara sabili da shi ba sani ba sabo ne, zai iya yabonka yau gobe kuma kaji wani abun daban.
Wasu suna ganin cewa wakar Rarara da ya saki to da wani babba a cikin jiga-jigan APC na jihar Kano yake, duba da cewa dai dama labari ya bazu kan cewar ba’a sanya sunan shi a mawakan Tinubu ba na yakin neman zaben 2023.
Wannan dai ba shi bane karo na farko da mawakin ke yin waka ta zambo musamman ga wadanda ba jam’iyyar su daya ba.
Ko a can baya ya sha yin wakoki da dama na zambo da ake ganin cewa da wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar Kano yake.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa
Ga wakar nan a kasa domin ku saurara.