Advertisement
Labaran Hausa

Yadda Na Haifi Yara 11 Dukkansu Masu Lalurar Makafinta Kuma Nake Kula Dasu Ni Daya

Yadda Na Haifi Yara 11 Dukkansu Masu Lalurar Makafinta Kuma Nake Kula Dasu Ni Daya

Wata mata ta bayyana a wani bidiyo a YouTube ta bayyana yadda ta haifi yara 11 wadanda duk makafi ne duk da ma’aikatan lafiya sun tabbatar mata da lafiyarsu lokacin su na ciki, Legit.ng ta ruwaito.

Matar wacce mijinta ya rasu yayin da ya barta ita kadai ta bayyana yadda take fadi-tashi tana kulawa da su yadda ya dace. Bidiyon Agnes Nespondi, wata ‘yar kasar Kenya, wacce ta haifi yara 11 kuma duk makafi ne tun bayan ta haife su, tabbas bidiyon ya dauki hankulan mutane da dama.

Bidiyon mai minti 8 da sakan 10 wanda shafin Afrimax English ta ruwaito ya nuna yadda matar ke kokari don tallafa wa yaranta. Agnes ta ce duk a makafi ta haifi yaranta duk da likitoci sun tabbatar mata da cewa babu wata matsala a lokacin da fake da cikinsu.

Daya daga cikin yaran nata har ya yi aure yana da yara ma. Matarsa ce wacce ko fafutukar ganin ta tallafa wa yaran. Mahaifiyarsa ta yi matukar wahala tun bayan rasuwar miji ya a lokacin yana da shekaru 90 da doriya. Mutane da dama sun tausaya mata har da masu hawaye.

Kalli bidiyan anan

 

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun Kalli wannan bidiyan zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button