Advertisement
Labaran Hausa

Yadda nayi lalata da maza sama da 500 domin na sami kudin da zan tsallaka Turai, cewar wata budurwa

Yadda nayi lalata da maza sama da 500 domin na sami kudin da zan tsallaka Turai, cewar wata budurwa

Wata matashiyar budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana wahalhalun da ta sha a kan hanyar tafiya cirani zuwa nahiyar Turai.

Matashiyar budurwar ta fito ne daga jihar Delta a yankin Kudu maso Kuduna Najeriya, sannan tana sana’ar gyaran gashi.

A wata tattaunawa da BBC Hausa tayi da budurwar ta bayyana cewa, wani mai safarar mutane ne ya yaudareta cewa yana da ‘yar uwa mai gyaran gashi a Turai, sannan Turawa na son yadda ‘yan Najeriya ke gyaran gashi.

Ta dai fada a hannun masu safarar mutane tana da shekara 20 a shekarar 2016.

Ta fiyarmu ta Nijar ta fara daga Nijar ne, mun bi ruwa mun bi rana mun shiga sahara kuma mun kusa kwashe wata guda cikinta.

Wani buzu ne ya kwashe mu a motarsa, muka dauki hanya banda akwai sauran kwana da tuntuni na mutu a wannan saharar, motar da muka shiga muna da yawa mun kai 20 maza da mata a kwance a cikin but din motar.

A kwance muke kafada da kafada, wasu
mutane dake cikin saharan sun tsayar da mu suka tambayi direban su waye a cikin
motar, direban yace tinkiyoyi ne a ciki a
raina nace ohh wani nice tinkiya.

Daga karshe sun samu nasarar tsallakawa kasar Aljeriya a wani gari da ake kira Oran.

A Aljeriya akwai inda ake jibge ‘yan cirani domin fakar idon jami’ai masu kula da shige da fice sai a tsallaka dasu kasar Morocco.

Budurwar ta bayyana cewa, sun fuskanci cin zarafi sosai a sansanin da aka ajiye su a kasar Aljeriya, inda maza ke shigowa suna amfani da su.

Wasu daga cikin mazan dake amfani da su suna dauke da cutar kanjamau, a kan idon su wasu daga cikin mazan suka mutu masu dauke da cutar ta kanjamau.

Bayan isar su Morocco ta nemi da ta gudu amma sai dai an gaya mata cewa, sai dai ta fanshi kanta wanda hakan ya sanya ta fara karuwanci don tara kudaden.

Da aka kai ni Morocco sai na nemi na kama gabana a Casablanca sai aka ce ai bani da yancin tafiya sabida ana bi na bashi, matar da ta biya kudi aka yi jigila da ni daga Najeriya Zuwa.

Dirham D30,000 kwatankwacin yuro €4,000 ake nema daga hannuna sune kudin jigilar, bani da yadda zan yi na sami wadannan kudin don haka bani da wani zabi sai dai nayi karuwanci.

Sai da budurwar tayi zaman gidan na kusan akalla shekara biyu da rabi kafin ta iya biyan kudin da ake binta.

Ta bayyana cewa, idan za’a kwana D300 ake biyanta sannan idan kuma kwanciyar ta dan lokaci ce D200 ake biya, kuma ko kudin kwana mutum ya biya sau biyu kawai zai kwanta da ita a cikin daren.

Sai dai a halin da ake ciki yanzu budurwar bata samu ta kai inda take son zuwa ba, sannan kuma a inda take makale yanzu bata samun wani abin azo a gani wanda zata nuna a matsayin riba idan ta koma gida.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button