Advertisement
Labaran Hausa
Trending

Yadda Tsohon Mijina Ya Yashe Albarkatun Jikina Na Mokade Tamkar Tsohuwa

Yadda Tsohon Mijina Ya Yashe Albarkatun Jikina Na Mokade Tamkar Tsohuwa

Wata mata ta bayyana yadda gabadaya ta sauya bayan rabuwar aurenta da tsohon nmijinta wanda su ka kwashe shekaru 18 takwas.

Matar mai shekaru 42 ta wallafa hotunanta wanda yanzu ta fara dawowa da gwabinta, LIB ta ruwaito.

A shekarar 20220 su ka rabu, yanzu kuwa ta koma shar kamar ba ita bace a baya.Cikin shekaru har ta dawo da kumarinta.

Matar mai yara biyu ta koma tana motsa jiki tare da neman abinci mai gina jiki. A cewarta yanzu maza har rububinta idan ta fita.

A cewarta:

“A baya na koma tamkar tanko na tsotse duk na sukurkuce, amma yanzu ina more rayuwa. ina cikin farinciki kuma na sauya.”

Sun yi aure ne a shekarar 2000, lokacin tana da shekaru 22. A cewarta ta fara shiga tashin hankali ne shekaru da dama da su ka gabata.

A shekarar 2021 su ka karkara rabuwa, a watan Oktoba su ka guntule gabadaya. Ta ce bayan rabuwarsu ta sauya sutturu ta siyo masu kyau.

Ta fara kwalliya sannan ta dena shan kayan shaye-shaye na hayaki.

Ta ce ta koma cin kwai da dankalin turawa tare da cin kaji da sauran kayan dadi.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button