
Yadda Wani Basarake Sai Yi Wuff Da Mata 6 Gobe A Lokaci Guda
Yadda Wani Basarake Sai Yi Wuff Da Mata 6 Gobe A Lokaci Guda
Wani Labari Da Muka Samu Yanzu Shine Ta Yadda Wani Basarake Zai Angwance Da Mata Shida A Gobe Kamar Yadda Shafin Daily News Hausa Suka Rawaito
Ooni na Ife zai auri mata ta 6 gobe
Ooni na Ife, Oba Enitan Ogunwusi, zai angwance da mata ta shida, Temitope Adesegun, a gobe Litinin, 24 ga Oktoba, 2022.
Jaridar Punch ta rawaito cewa sanarwar ta fito ne daga mai magana da yawun Ooni, Moses Olafare, a cikin wani sakon Facebook da ga wallafa a yau Lahadi.
A ranar Alhamis, 20 ga Oktoba, 2022 me dai Sarkin ya auri matarsa ta biyar kuma wa ce ta kafa dandalin Makon Kwalliya na Afirka, Ronke Ademiluyi wacce ita ce jikanyar Ooni na Ife na 48, Ajagun Ademiluyi.
A cewar Olafare, matar Ooni ta shida mai jiran gado, Adesegun, gimbiya ce wacce ta fito daga yankin Ijebu.
A cikin sakon Facebook, Olafare ya rubuta, “Olori Temitope Adesegun Ogunwusi an Ijebu Princess cum Ile-Ife Queen.
Bayan aurensa da Naomi Silekunola a watan Disamba 2021, sarkin ya auri mata biyar cikin kasa da watanni biyu.
Matan nasa su ne; Mariam Anako, wanda yanzu ita ce matarsa, Satumba 6, 2022; Elizabeth Akinmudai; Tobiloba Philips, Oktoba 9, 2022, Ashley Adegoke, Oktoba 14, 2022 da Ronke Ademiluyi, Oktoba 20, 2022.