
Yadda Wani Dan Mafarauchi Ya Kashe Ganinsa Yayin Da Yake Gwadin Maganin Bindiga
Yadda Wani Dan Mafarauchi Ya Kashe Ganinsa Yayin Da Yake Gwadin Maganin Bindiga
Wani Labari Da Ya Riskemu Yanzu Shine Ta Yadda Wani Dangida Mafarauchi Yayi Sanadiyyar Mutuwar Kaninsa Yayin Da Yayi Gwadin Maganin Bindiga A Jikinsa Kamar Yadda Shafin Daily News Hausa Suka Wallafa
‘Ɗan wani mafarauci ya kashe ƙaninsa yayin gwajin maganin bindiga a Kwara
A jiya Lahadi ne wani ɗan mafarauci a garin Dutse Gogo da ke kusa da Kaiama, shelkwatar karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara, Abubakar Abubakar, ya harbe ƙaninsa mai suna Yusuf Abubakar a lokacin da yake gwada ingancin wata sabuwar laya ta kariya daga harbin bindiga da mahaifinsu ya siyo.
Mafaraucin, Abubakar Abubakar, wanda ke zaune a garin Dutse Gogo kuma mahaifin ‘ya’yan biyu ya sayo wata laya ta kariya daga harbin bindiga, inda ya so ya tabbatar da ingancinta ta hanyar amfani da ‘ya’yansa maza kafin ya fara amfani da wannan laya.
Majiyoyi sun bayyana cewa, yayin gwajin layar, marigayin ya daura layar, inda shi kuma ƴaƴan nasa da ke riƙe da bindigar mahaifinsu ya ɗirka masa, yayin da nan da nan ta kama Yusuf, ɗan shekara 12 ya kuma fadi kasa ya rasu man take.
An kuma tattaro cewa da sanin cewa laya ta gaza kuma kanin nasa ya mutu, Abubakar wanda babban kanin nasa ne ya tsere ya ruga cikin daji.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ‘yan sandan sun fara gudanar da bincike tare da farautar babban dan uwan da ya harba bindigar’
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.