
Yadda wani magidanci inginiya ya gina gida sukutum da mai daki 3 da gororin roba guda 14,800
Yadda wani magidanci inginiya ya gina gida sukutum da mai daki 3 da gororin roba guda 14,800
Injiniya Yahaya Ahmed Injiniyan daya gina gida a Kaduna inda ya yi amfani da gororin roba guda 14,800 a matsayin bulo. Kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
Premium Times ta rahoto cewa, Ahmed shine daraktan wata kungiya mai zaman kanta “Developmental Association of Renewable Energies in Nigeria”.
Legit.ng ta tattaro cewa, injiniyan yace kungiyarsa ta gina gidan ne domin karfafa sarrafa kayan da basuda amfani tare da samar da ayyukan yi a Najeriya.
Da yake bayyana tsarin ginin gidan Ahmed yace, ma’aikatan sun cika kwalaben robobin da yashi tare da dai-daita su ta hanyar hada su da igiyoyi.
Sannan yace, ginin shi ne irinsa na farko a yankin kudu inda yace yafi arha gina shi sabida ana samun kayayyakin gini a kan tituna da wuraren zubar da shara.
Gidan yanada dakuna uku bandaki da kicin, tafuskar karfi da karko Ahmed ya ce gidan yafi gidajen bulo karko kuma zai iya dauwama sama da shekaru 300 idan an gina shi yadda ya kamata kuma a tsanake.
Acewar sa, wuta ba zai iya cinye shi ba harsa shi ba zai iya huda shi ba, kuma yana iya jure girgizar kasa.
Ya dace da kowane irin sauye-sauyen yanayi Ahmed yace, duk wanda keda fasahar gini za’a iya amfani da shi a matsayin aiki wajen gina gida, yakara da cewa kungiyarsa ta horar da matasa da dama.
Ahmed yace, sun fara wannan aikin ne don rage yawan robobin dake gurbata muhalli da haddasa cututtuka.
A martanin da ya mayar dangane da shirin ginin, mataimakin daraktan masu ba darahotanni kan yanayin Afirka “Piman Hoffman” ya bukaci gwamnatin Najeriya data tallafa wa kamfanonin dake sabunta kayyaki domin ceto al’ummar kasar daga barazanar gurbatar yanayi.
Ya yi nuni da cewa, robobi babbar barazana ce ga wanzuwar mutane, dabbobi da dukkan halittu masu rai.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa