Advertisement
Labaran Hausa

Yadda wani magidanci ya yiwa matarsa dukan kawo wuka har sai da ya kashe ta akan burodi

Yadda wani magidanci ya yiwa matarsa dukan kawo wuka har sai da ya kashe ta akan burodi

Gwamnati jihar Anambra za ta gudanar da bincike kan yadda wani magidanci mai suna Wilson Uwadiegwu ya kashe matarsa da dukan tsiya saboda buredi.

Kwamishinan harkokin mata na jihar Ify Obinabo ta sanar da haka a garin Awka ranar Laraba bayan mahaifiyar mamaciyar Cordelia Anene ta kawo wa kwamishinan ziyara a ofishin ta, kamar yadda shafin “Hausaloaded” suka ruwaito.

A wani bidiyo da ya kareda shafukan sada zumunta a yanar gizo ya nuna Uwadiegwu ya kashe matarsa Ogochukwu Anene wacce aka fi sani da ‘Ada Awka’ da dukan tsiya bayan ta cinye buredi da ya siyo domin karin kumallo.

Cordelia ta ce Uwadiegwu ya lakada wa Ogochukwu dukan tsiya saboda yara sun zo sun tambayeshi buredin da za su yi karin kummalo da shi.

Bayan kwanaki biyu da Uwadiegwu ya yi wa matarsa duka ne aka kwantar da Ogochukwu a asibiti inda daga nan ta ce ga garin kunan.

Sakamakon gwajin da likitoci suka yi ya nuna cewa Ogochukwu ta rasu a dalilin raunin da ta ji a cikin jikinta saboda dukan da aka yi mata.

Tun da Uwadiegwu ya lakada wa matarsa duka ya gudu ba a sa sake ganin sa ba har yanzu, Cordelia ta yi kira ga gwamnati da ta kwato wa ‘yarta haki.

Bayan haka Obinabo ta ce ma’aikatar kula da al’amuran mata za ta hada hannu da gwamnati domin ganin an bi mata hakki.

Source of “Hausaloaded

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button