Advertisement
Labaran Hausa

Yadda wani matashi mai suna Faisal ya kera Keke Napep da kansa a jihar Kano

Yadda wani matashi mai suna Faisal ya kera Keke Napep da kansa a jihar Kano

Wani fasihin matashi mai suna Faisal ya kera keke napep wacce ake kira da sunaye daban-daban da suka hada da a dai-daita sahu, kurkura, kafi babur, tuk-tuk, keke da dai sauransu.

Matashin wanda dan asalin karamar hukumar Dala ne ya wallafa hotunan wannan sabuwar kirkira ta fasaha da yayi a shafinsa na facebook mai suna Faisal Art a ranar Alhamis din nan data gabata, inda ya nuna hotunan daga inda ya fara har zuwa karshe.

Bayyanar wadannan hotuna na keke napep da wannan matashi ya kera sun yadu cikin gaggawa musamman madai a shafukan sada zumunta da kuma manyan jaridu na gida dama na wajen Najeriya, mutane da dama sun yaba da kokarin wannan hazikin matashi.

Wani daga cikin abokanan Faisal mai suna Mustapha Sani Bala ya bayyana cewa, tun a lokacin da suke karatu a makarantar firamare ta Dantata Primary School, Allah yayi ma Faisal basirar zane dama sauran abubuwa naban mamaki.

Haka nan ma har suka zo sakandare wato sakandiren gwamanti dake Gwammaja, basirar wannan matashi sai dada karuwa take.

Ya kara da cewa, akwai wani lokaci a GSS Gwammaja lokacin suna da dan karancin malamai, a lokacin da sauran dalibai suka shagaltu da surutu shi kuma Faisal ya maida hankali wajen zana duka makarantar da kuma taswirarta.

Duk da kasancewar Faisal ba dalibin fasaha da kimiyya ba hakan bai sare mishi gwuiwa ba wajen cimma muradun shi, tunda gashi a yanzu haka ya kera keke napep samfurin Kano.

Najeriya dai kasa ce da Allah ya albarka ce ta da al’umma masu fasahohi daban-daban, inda ko a kwanakin baya sai da aka samu wani matashi da ya kera mota mai amfani da hasken rana a garin Maiduguri.

Haka nan ma an sha samin matasa da suka yi abubuwa na al’ajabi, abubuwan da in aka tattale su zasu iya zama kari a cikin hanyoyin da kasar zata rika samin makudan kudaden shiga.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Ga hotunan a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button