Advertisement
Labaran Hausa

Yadda wani matashi ya sanya aka yanka hannunsa domin rubuta sunan masoyiyarsa

Yadda wani matashi ya sanya aka yanka hannunsa domin rubuta sunan masoyiyarsa

Masoya da dama na iya aiwatar da abubuwa daban-daban domin nunawa abun kaunar su irin tsantsar son da suke musu.

Wasu abubuwan da masoya ke yi a wasu lokutan na domin nuna irin son da suke wa abun kaunar nasu na matukar daurewa mutane kai, kamar yadda shafin “Hausaloaded” suka ruwauto.

Hakan shine abinda ya faru da wani matashi wanda ya sanya aka yanka fatar jikin sa aka rubuta sunan masoyiyar sa.

A wani bidiyo da shafin “Linda Ikeji ya sanya ya nuna matashin wanda yake sana’ar siyar da kayan dauke da sunan masoyiyar tasa rubuce a hannun sa.

A cikin bidiyon an nuna matashin tsaye a cikin wurin sana’ar sa ga kuma kayan miyar sa nan a wurin, daga nan sai kyamarar daukar bidiyon ta zuko domin nuna yadda aka rubuta sunan Zainab radau rubuce a hannun sa.

Yankar da akayi masa wajen rubutun dai sabuwa ce domin a na iya ganin jini a jikinta, sannan kuma bai rufe wajen da bandeji ba domin hana wasu kwayoyin cuta shiga ciki.

Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button