Advertisement
Labaran Hausa

Yadda wani matashi yayi ta sharbar kuka sabida anki daukan sa aiki a Banki bayan mummunar wallafar da yayi a kan su

Yadda wani matashi yayi ta sharbar kuka sabida anki daukan sa aiki a Banki bayan mummunar wallafar da yayi a kan su

Wani matashi ya koka bayan bankin Zenith sun ki amincewa su tattauna da shi sabida wata wallafar da yayi shekaru 2 da suka gabata yana sukar bankin, kaamr yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.

A cewar mutumin, yayin da yaje a tattauna da shi wurin aikin, wata mata daga bangaren HR ta nuna masa wata wallafa da yayi shekaru biyu da suka gabata.

Wannan dalilin yasa ya bukaci mutane da suyi taka-tsantsan akan abubuwan da suke wallafawa a shafukan su.

Matashin mai amfani da suna @djbantibenl ta bayyana artabun da suka yi bayan Zenith Bank sun ki bashi gurbin aiki sabida wani wallafa da yayi a Twitter shekaru biyu da suka gabata.

Ya yi wallafar ne shekarar 2020 wacce ta ja masa asarar babban aikin da ya kusa samu.

Ya bayyana nadamar sa akan wallafar inda ya dinga kuka tamkar jariri.

A cewarsa: Naje wata tattaunawa ta neman aiki a bankin Zenith, wata mata daga HR ta shigo inda ta nuna min wata wallafa da nayi tun shekarar 2020.

A wallafar ya kira bankin Zenith da banki mara amfani a gaba daya Afirka, a cewar sa ya koyi darasi mafi girma a rayuwarsa.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button