
Yadda Wata Budurwa Ta Bude Guruf Na Whatsapp Ta Saka Samarinta Domin Ta Gaya Musu Zatayi Aure
Yadda Wata Budurwa Ta Bude Guruf Na Whatsapp Ta Saka Samarinta Domin Ta Gaya Musu Zatayi Aure
Wani matashi dan Najeriya ya bayyana yadda budurwarsa ta yaudare shi a wani rahoto da jaridar Legit.ng ta wallafa.
Saurayin mai suna Prince Mudi yace budurwar ta bude sabon dandali (Group) a Whatsapp sannan ta saka shi a ciki
Amma sabon Guruf din da ta bude ya kunshi baki daya samarinta saboda tana son hada sua wuri guda.
Sai dai manufarta a zuciya shi ne tana son rabuwa da su baki daya kana ta ci gaba da rayuwarta da sabon saurayin da zata aura.
Meyasa ta rabu da samarin baki daya?
Prince Mudi ya ci gaba da cewa bayan ta gama tattara su sai ta sanar musu cewa aure zata yi.
Daga nan kuma ta fice daga Guruf din. Prince Mudi yace:
A 2017 na yi soyayya da wata yarinya tsawon shekara daya.
Wata rana kawai ta saka ni a Guruf din Whatsapp tace Ku ne mutanen da bana so kuma komai ya zo karshe saboda zan yi aure karshen mako mai zuwa.”
“Ba wata-wata ta fice daga Guruf din ta barmu nan muna kokarin sanin juna.”
Mutane sun yi martani
@ohlynxx93 yace
Abun jin dadin shi ne mai yuwuwa diyarta ce zata sha wahata ta girbi laifin da mahaifiyarta ta tafka.”
@the saitmusty yace:
“Haba ku bar komai kowa ya cire kudi ya siyo sabon kaya, ku hałarci bikinta a matsayin kawayen amarya.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.