Advertisement
Labaran Hausa

Yadda wata budurwa ta haifi jarirai 5 a lokaci guda bayan kuma bata taba aure ba

Yadda wata budurwa ta haifi jarirai 5 a lokaci guda bayan kuma bata taba aure ba

Oluomachi Linda Nwojo, dalibar ajin karshe a jami’ar noma ta Okpara, Umudike ta haifi yara biyara lokaci guda da kanta kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.

Budurwar wacce ‘yar asalin karamar hukumar Ohafia dake jihar Abia ce ta haifi yara mata guda uku da kuma maza biyu a ranar Litinin da misalin karfe 9:02 na dare.

Ta haihu ne a asibitin tarayya na Umuahia dake jihar Abia wanda wannan ne karo na farko da a tarihin asibitin aka taba amsar haihuwar ‘yan hudu.

A wata tattaunawa da wakilin Legit.ng yayi da matar ta bayyana cewa, bata taba aure ba.

A ranar Talata, wani Prince Krux ya bayyana hotonta da jariran data haifa inda yace matarsace.

Amma a tattaunawar da wakilin Legit.ng yayi da ita tace, bata taba aure ba, nan da nan mutane suka dinga tsokaci iri-iri karkashin wallafar.

Ga kadan daga cikin mutanen da suka tofa albarkacin bakin su a karkashin wallafar.

Nkameme Ogechi Caroline tace: Wannan kyautar Ubangiji ce muna fatan duk inda uban yaran nan yake yazo ya riki yaran da mahaifiyar su, abin ban al’ajabi ne.

Prince Steven yace: Kuma bata taba aure ba? To waye yayi mata cikin? Ya kamata wanda yayi mata wannan aikin ya cigaba daga inda ya tsaya. Muna mata fatan
alkhairi.

Nkechi Okanu Omorogbe tace: Gaskya Ubangiji yayi mata baiwa, muna ta samu taimako, yaran da nahaifa guda biyar daban-daban sune Ubangiji ya ba wata a lokaci guda.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button