Advertisement
Labaran Hausa

Yadda wata mata ta auri Maza 2 ba tare da sanin su har asirinta ya tonu suka gane

Yadda wata mata ta auri Maza 2 ba tare da sanin su har asirinta ya tonu suka gane

Labarin wata mata mai suna Acheingdai da ta auri maza guda biyu ba tareda dayansu ya san da daya ba, ya karade kafafen sadarwa na zamani.

Matar kuma ta cigaba da rayuwar ta ba tare da sun gano da hakan ba, daya daga cikin su bai iya ganowa cewa matar tana da wani mijin daban bayan shi ba, har sai ranar da suka hadu a kan hanya kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.

Motar tace ta tsorata a yayin da daya mijin ya ari motar da nufin ya dan je ya dawo, fitar shi ke da wuya sai yayi kacibus da wani mai gadi wanda ya shaida mishi cewa lallai wannan motar da yake akai ta matar shi ce.

Mai gadin ya fito da wayar sa inda ya nuna masa hotunan ta, wanda a nan take ya tabbatar da cewa lallai matar tashi ce, kuma daga nan ne ya gano cewa su biyu take aure ba shi kadai ba.

Matar ta riga da ta tsara yanda take haduwa da mazajen guda biyu, daya a cikin ranakun aiki a yayin da dayan kuma take haduwa da shi a ranakun karshen mako.

Matar tayi musu karya ne ta yadda asirin nata bazai tonu ba atunanin ta, Mijin ya wallafa a shafin sa na tuwita.

Mijin mai suna Mjengoke ne ya wallafa labarin a shafin shi na tuwita, ya wallafa rubutun kamar haka:

Kawai ka dan aro motar matarka zaka dan zagaya a cikin gari, kawai daga fakawar ka sai kaga wani mutum yazo yana tambayar ka cewar me kake yi da motar matar shi?.

Ka fada mishi cewa, motar ai ta matarka ce amma sai kawai ya kaika ofishin sa inda ya nuna maka takardun motar.

Alhalin ita matar a can baya ta fada maka cewa bashi taci a can wajan aikinsu ta sayi motar.

Ka nemi ya nuna maka hoton matar tashi sai ya nuna maka, kwatsam hoton daya ne da na matarka wacce kuka haifi ‘yaya biyu tare da ita.

Tayi mishi karyar tana aiki a wani kamfani a karshen mako ne kawai suke haduwa, alhalin kai kuma matar taka tayi maka karyar cewa tana zuwa karatu ne na masta digiri din ta a wata jami’a a wannan karshen makon, har na tsawon shekara daya.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button