Advertisement
Labaran Hausa

Yadda wata mata tayi fashi a cikin banki da bindigar roba

Yadda wata mata tayi fashi a cikin banki da bindigar roba

A watan Satumbar 2022 daya gabata ne aka samu wata mata da taje banki da bindigar roba inda ta daga ta sama da zummar ta cire kudaden ta daga asusun ajiyar ta na bankin da suka kai $12000.

Matar mai suna Sali Hafiz ‘yar kasar Lebanon mai shekaru 28 tace, tayi hakan ne domin cirar kudi daga asusun ta, wanda tace zata yi amfani dasu ne wajen biyan kudin maganin ‘yar uwarta dake fama da ciwon sankara kamar yadda.

A wani dan gajeren bidiyo da yayi yawo a shafukan sada zumunta anga Sali Hafiz a cikin banki ta zaro bindiga wacce tayi ma ma’aikatan bankin barazana, inda daga nan ne aka ga suna ta kirgo kudade suna bata.

A kasar ta Lebanon $Dala 200 zuwa da 400 ne kawai bankuna ke ba ‘yan kasar damar iya cirewa a kowanne wata domin amfanin su na yau da kullum.

Hakan ya samo asali ne daga barazanar tattalin arziki da kasar ke fuskanta wacce ta jefa uku bisa hudu na ‘yan kasar cikin talauci.

Sali Hafiz dai ta kutsa kai cikin banki tare da wasu mazaje, sannan kuma ta kutsa zuwa inda ake bada kudi inda daga nan ne ta zato bindigar robar da tayi barazanar da ita wajen amsar kudaden nata data ce zata biya maganin ‘yar uwarta da su.

A bidiyo na kai tsaye data yada a shafinta na facebook Saki Hafiz ta bayyana cewa, bata shiga banki don ta kashe kowa ba ko ta sanya ma bankin wuta ba, tace taje ne domin ta karbi hakkinta.

A ‘yan kwanakin nan dai a kasar ta Lebanon ana yawan samun mutane dake yima ma’aikatan banki barazana wajen cirar kudaden dake ajiye a asusun su, tace bindigar kuma da tazo da ita ta roba ce.

‘yan sanda sun neme ta ruwa a jallo tace bankin ne ya tursasa ta yin hakan, inda tace taje bankin da zumar cirar kudi da yawa domin biyan kudin maganin ‘yar uwarta, sai dai tace bankin sun fada mata cewa $Dala 200 kawai zata iya cirewa a duk wata.

Bayan faruwar lamarin, Sali Hafiz tayi ta yin wasan buya da jami’an tsaron kasar inda daga bisani kuma ta mika kanta gare su.

An kaita kotu inda aka caje ta kudin kasar ta Lebanon fam dari shida, sannan kuma kotu ta hana ta damar fita kasar waje har na tsawon watanni shida.

Rahoto daga👉 Labarun Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button