Advertisement
Magunguna

Yadda za’a magance ko wacce irin matsala ta kankancewar mazakuta da saurin kawowa yayin saduwa da iyali

Yadda za’a magance ko wacce irin matsala ta kankancewar mazakuta da saurin kawowa yayin saduwa da iyali

MATSALAR KANKANCEWAR GABA WATO AZZAKARI.

Kasancewar citta nau’in iccene mai daraja wanda mutanen sin suka shahara da iya sarrafasa kuma duk wani nau’in magani na sa sha’awa ko karata da ita ake amfani.

Don haka ana daka citta agaurayata da garin kastul hindi sai azuba zuma da man kanumfari amotse su,sai arika shan babban cokali 3 sau 3, arana, amma za’ayi sati biyu anasha ko fin haka gwargadon girmanda ake bukatar gaban yayi.

Sannan ayawaita shafa man tafarnuwa agaba duka kewayensa.

Ana samun kwan salwa afashe cikin kofi,sai azuba zuma da garin citta kadan akadasu sosai za’ayi hakan gab kwanciya, ana sha akwanta, amma adan motsa jiki.

Sannan adanyi gudu(exercise) koda na 10min ne akalla ayi hakan tsawon week guda.

Asamu man kanumfari da garin h/sauda da zuma da ridi sai azuba zuma kwatankwacin robar yoghurt sai garin habbus sauda rabin ledarsa, sai man kanumfari rabin kwalbar sai a zuba ridin ba tare da an sarrafashiba ta soyawa ko makamancin hakan.

Azuba cokali 5, arika shan cokali 5, in za’akwanta safe da rana kuma cokali 2 ko 3 akarshe cin abinci,wannan yana magance saurin inzali dakuma kara girman gaba.

Ana dafa duma ko kabushi ta hanyar basu tsoro karsu dafu sai asauke amarkade azuba madara peak ashanye.

Inaso kuma ku sani yawan shekaru na taka muhimiyar rawa akan girma da karfin azzakarin namiji.

Domin ba yadda zaayi ace mutum yayi kamar yadda dan shekara sha takwas zai yi in yakai shekara 50 zuwa sama. ko da yake namiji zai iya ma mace ciki kome tsufansa.

Amma mace da zaran ta kai menopouse to ita da haiwawa to sai dai wani ikon Allah. Akwai wani bawon itace da ake kira dan kamaru in aka same shi a hada da jar kanwa kadan a tauna a hade ruwan. a gaskiya indai na kwaran aka samu zaa ga biyan bukata.

Dangane damatsalar kankancewar gaba,kamar dayawa akwai likitoci dadama dasukayi bayanai akai dakuma matsalolin dasukan jawo hakan,amma ni bayanin dazanyi anan kawai shine hanayar magance hakan.

Akwai magunguna kamar haka wadanda za’aiya amfani dasu insha Allahu gaba yakara tsayi dakuma kauri, dama karfi, za’a iya samo zaitul karua, da man Hulba, man Habba ahadasu yawan daidai da daidai,arika shafawa,akowanne lokaci, mussaman kamar da daddare da kuma safe, in sha Allah idan akadau lokaci ana yi za’ayi mamaki.

Sannan za’a iya samo garin fijil da zuma amma yadda zaa hada shine idan aka samo zumar sai adorata akan wuta mara karfi, idan tadan dahu, sai a sauketa a zuba fijil din, sannan a kara dorasu a hade, sannan a sauke a rika amfani dashi wajan sha kamar sau uku a rana in sha Allah gaba zai kara kauri da kuma karfi.

Bayan haka za’a iya samo Galic capsult, wato capsul na tafarnuwa a rika shansa kwaya dai-dai, ko kuma bi-biyu in sha Allah za’a dace, domin wannan anjarraba shi kuma yayi aiki sosai.

Idan ba’a sami capsult dinba to sai a rika amfani da Galic oil, a rika shansa ati ko kuma ruwan dumi shima zaiyi, amma fa idan da za’a sami cpsult yafi.

Allah ya bamu sa’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button