Advertisement
Magunguna

Yadda zaku magance abubuwan da suke kawo raunin mazakuta

Yadda zaku magance abubuwan da suke kawo raunin mazakuta

Sakamakon bincike da wasu likitoci suka gano a kasar Amurka ya nuna cewa cutar siga wanda ake kira ‘Diabetes II’ na rage karfin azzakarin namiji.

Likitocin sun gano haka ne a binciken da suka gudanar a kan mutane miliyan 30 a kasar Amurka.

Sakamakon da binciken da wadannan likitoci suka yi ya nuna cewa mai dauke da cutar na tattare da matsalolin cututtukan dake kama zuciya da cututtukan dake kama huhu wanda hakan kadai na iya rage karfin gaban namiji.

Bayan haka wani malami a jami’ar Legas dake koyarwa a sashen koyar da aikin likita, Ifedayo Odeniyi, yace cutar siga na kama mutum ne idan aka samu matsala da wasu daga cikin ababen da ke sarrafa abincin da muke ci a cikin mu.

Shi Insulin ya na aiki ne a jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar wa mutum kuzarin da yake bukata a jiki.

Ya kuma kara da cewa rashin aikin sa ‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da cutar siga.

Bayan haka kuma ya yi kira ga mutane da su yi watsi da camfin da ake yi wai shan zaki ne ke kawo cutar siga, yace hakan ba gaskiya bane.

Likita ya ce saboda irin wannan camfe-camfe ne ya sa mutane ke hana kansu cin abinda ya kamata don samun kuzarin da suke bukata a jikin su.

Ya ce tabas yana da mahimmanci idan mai dauke da cutar siga na kiyaye sharuddan da ya shafi irin abincin da ya kamata ya ci, amma haka ba yana nufin kada mutum ya hana kan sa cin abincin da ke da sinadarin ‘Carbonhydrates’ saboda samun kuzari a jikin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button