
Yadda zaku magance matsalar kankancewar azzakari lokacin da sha’awarku bata tashi ba
Yadda zaku magance matsalar kankancewar azzakari lokacin da sha'awarku bata tashi ba
A cikin Azzakari akwai wasu jijiyoyin jini da ake kira da Arteries da veins suna shigar da jini cikin Azzakri da fitar dashi daga azzakari.
Wadannan jijiyoyin jini suna taka muhimmiyar rawa wajen Tsayawar Azzakari(Erection)wanda da wasa suka dena aiki Azzakarin ka ya dena aiki kenan.
A lokacin mikewar Azzakari, jijiyar arteries Suna kara girma don ƙara yawan jini zuwa azzakari, Jini yana cika bututu guda biyu na nama wanda suke da taushi a cikin azzakari,ana ce dadu (corpus cavernosa).
Wannan yana sa su kumbura su kara girma, suna sa azzakari ya zama babba kuma ya yi karfi.
Bayan mutumya fitar da maniyyi ko kuma ya daina jin sha’awar jima’i, sai jijiyoyin jikin su faɗaɗa kuma tarkon jinin ya koma cikin jiki. Azzakari ya dawo daidai gwargwado ya zama bashi da karfi saboda jini ya fita daga cikin sa.
Saboda haka wadan da suke damuwa don Azzakarin su ya zama karami lokacin da babu Shaawa wannan ba komai bane,haka abun yake dama.
Amma akwai masu fama da matsala ta Erectile dysfunction (ED) wadan da basa iya tsayar da azzakari na wani lokacin, ma’ana da Azzakarin ya mike lokaci kadan sai ya kwanta.
Wadan nan sune suke da matsala daya kamata su nemi magani akan ta,akwai abubuwa da yawa da suke jawo wannan matsala ita ma dabida haka ku kasance damu insha Allah zamu kawo bayani akan hakan.
Duk wanda yake fama da wannan matsala ta rashin dogon zango ko saurin kawowa yayi kokari yayi wannan hadin.
Zaka samu itacen rigas doka,zaka samu itacen dan kamaru,zaka samu saiwar kizaki zaka hade su wane daya amma ana so a daka su ne,idan danye ne ka samu ba matsala sai a rika dafawa.
Idan bushashshe ne zaka hade su waje daya daidai gwargwado kowanne,amma dan kamaru ya zama kwata din adadin su(rabin rabin adadin su) sai a dake su a rika shan rabin karamin chokali (teaspoon ana zubawa a ruwan shayi ba madara sau 2 a rana amma a tabbata anci abinci kafin asha na tsawon kwana 10.
Idan kuma danye ka samu ana dafawa ne a rika shan karamin kofi sau 2 a rana shima na kwana 10, amma Banda yara banda mara aure.