
‘Yan sanda sun kama wani barawo bayan yayi basaja ya sato makudan kudade wanda aka tara a coci
'Yan sanda sun kama wani barawo bayan yayi basaja ya sato makudan kudade wanda aka tara a coci
‘Yan sanda a jihar Ekiti sun cafke wani barawo mai suna “Akindele Opeyemi Olugemi” mai shekara 32 wanda ya sace kudaden sadakar da aka tara a wata cocin jihar.
Wanda ake zargin yana tafiya ne akan babur dauke da jaka lokacin da aka tsayar da shi domin a duba shi.
Da farko yaki yarda a binciki abinda yake dauke da shi amma daga karshe ‘yan sanda sun yi masa ta karfi, kamar yadda shafin “Labarun Hausa” suka ruwaito.
Bayan anyi masa binciken kwakwaf an samu kudade a tattare da shi, koda aka masa tambayoyi bai bayar da gamsashshiyar amsa kan yadda ya sami kudin ba.
Binciken ‘yan sanda daga baya ya gano cewa, ya sato kudin ne daga cocin “Christ Apostolic Church Camp Ground” a Ikeji Ara-Ikeji jihar Osun.
Ya amsa laifin da ‘yan sanda ke tuhumar sa da shi inda yace, yayi aiki a matsayin mai gadi a cocin na tsawon shekara biyu, sannan yayi murabus a farkon shekarar nan.
Yayi basaja ya koma cocin domin yin addu’a cikin dare inda daga bisani ya lallaba yaje wurin ajiye kudin cocin yayi awon gaba da su.
Ko da aka kirga kudaden adadin su ya kai Naira dubu dari shida da dari daya da sha biyar (N600,115), ‘Yan sanda sun bayyana cewa za’a tura wanda ake zargin zuwa kotu tare da sauran masu aikata laifuka da hukumar ta tasa keyar su a jihar.
Rahoto daga👉 Labarun Hausa