
Yanzu yanzu: Wasu ‘yan Daba sun cinna wuta a gidan mawaki Kahutu Rarara
Yanzu yanzu: Wasu 'yan Daba sun cinna wuta a gidan mawaki Kahutu Rarara
Kasa da awa daya bayan sanar da
sakamakon zaben gwamnan jihar Kano, wasu ‘yan daba da ba’a san ko su wanene ba sun sanya wuta a gidan shahararren mawakin siyasan nan “Dauda Kahutu Rarara”.
Rarara dai ya karkata ne wajen yi wa jam’iyyar “All Progressives Congress” (APC) kamfen, inda ya yi wakoki a gangamin kamfen jam’iyyar daban-daban.
A cewar wani ganau wanda ya kasance
mazaunin yankin mai suna “Yusuf Abdullahi”, ‘yan daban sun farmaki gidan mawakin sannan suka fara lalata muhimman abubuwa kafin suka cinna wa gidan wuta.
Sai dai kuma ‘yan mintuna bayan nan an tattaro cewa, ‘yan sanda sun tarwatsa ‘yan daban amma dai wutar ta cigaba da ci yayin da ake jiran isowar yan kwana-kwana.
Abdullahi ya ce: Babu abun da kake jiyowa sai karar fashewar abubuwa daga gidan yayin da wutan ke cigaba da lalata kayayyaki.
Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.