
Yar Uwa Ga Hanyoyi Da Zaki Bi Ki Kare Kanki Daga Kamuwa Da Cutar Da Zata Lalata Miki Gabanki
Yar Uwa Ga Hanyoyi Da Zaki Bi Ki Kare Kanki Daga Kamuwa Da Cutar Da Zata Lalata Miki Gabanki
Hanyoyin Da Zaki Bi Domin Kare Kanki:
1- Avoid Vaginal Douching : A cikin Farji akoi wassu kwayoyin bakteriya wadanda basa cutarwa kuma sunada amfani , amfaninsu shine suna taimakawa wajen bada kariya ga Farji , sai kaga wassu matan sukan wanke Farji da Sabulu ko detol haka , wadannan abubuwanda ake amfani wajen wanke farji yakan kashe bakteriya masu amfani na Farji , Sai masu cutarwa su samu daman shiga. A kiyaye wanke Farji Da Sabulu dakuma wadansu abubuwa Wanda bamusan Kansu ba.
2- Uses of Underwear : Amfani da wandon pants , wassu matan sukan bar wandonsu yayi datti , Barin datti ko amfani pant masu datti yakan bawa kwayoyin cuta daman shiga Farji.
A Tsaftace wanduna.
3- Cleaning Faeces : wajen wanke bahaya mafi yawa mata sukan dauki kwayar cutar da take dubura zuwa Farji, wanda basa yiwa dubura illa amma sukan yiwa Farji illah.
Shawara shine afara wanke Farji kafin a wanke dubura.
4- Sharing of Underwear: amfani da pants na wassu , ta yiu wacce kuke amfani da pants daya tanada cutar Sanyi idan kinyi amfani da nata kema zaki iya dauka.
Sai a kiyaye.
5- Sexual intercourse : mutun yakan iya daukan wannan cutar lokocin saduwa da namiji shawara itace adinga amfanida Condom lokocin saduwa..
A Wani Bangaren Kuma Wani Tambaya Da Ake Mana..To Ga Amsar Nan
Shin Maganin Gyaran Nono Na Amfani?
Amsa;
Hakika baza ace basu aiki ba, domin matan da suke amfani da su suna ganin tasirinsu. Abinda suke yi shine suna kumbura tsoka da kitsen nonon ne kawai, sai aga ya kara girma.
Amma daga bisani suna iya haddasa cutar daji ko kuma wasu matsaloli a nono. Sa’annan kuma suna takure fatar nono ne sai a gansu sun cicciko sunyi tsattsaye.
Amma da zarar sun gama aikinsu (tunda ba dauwama zasu yi ba) sai fatar ta saki, kuma nonon ya kankance kuma ya sake zubewa.
Da wannan nake ganin ya kamata mata su guji amfani da su, kamar yadda manyan likitocin duniya suke bayar da shawara.
To Allah Ya Kyauta Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan Bayanin Zamu So Karben Ra’ayoyinku A Sahen Comment.