Advertisement
Magunguna

‘Yar uwata idan kina son kasancewa cikin dauwamammiyar ni’ima kibi wadannan hanyoyin

'Yar uwata idan kina son kasancewa cikin dauwamammiyar ni’ima kibi wadannan hanyoyin

Ki sami ganyen zogale ki wanke ki tabbatar babu datti saiki cocumber (gurji) ki fereshi ki yanyanka ki hada da ganyen Zogalen ki markade da blander saiki tace ruwan ,sai ki zuba madara da zuma aciki idan kinaso yayi sanyi ki saka a firij yayi sanyi lokacin shan ruwa kisha.

HADIN NI’IMA :

‘Ya’yan kankana
Danyen gyada Mai kyau
Dabino
Alkama
‘Ya’yan zogale

Sai ki hada ki dakesu gabadaya suyi laushi sosaii sai ki rinka Shan karamin cokali da Madara ta ruwa safe da yamma.

Bari mu fara da masu neman karin ‘Hips. ’ Ina son a fahimci cewa girman kugu halitta ce, wasu matan har kauce hanya suke yi, su je a saka musu kugun roba.

Kun ga akwai alamar kauce hanya a nan ke nan.

Akwai nau’in ababen da mace za ta rika ci, sannu a hankali, kyan diri da halittarta za su kara fitowa, ita ma za ta rika ji ta kara cika, ta yi kyau.

Masana a wannan fannin, sun bayar da
shawarwarin amfani da

– Abarba,
– Ayaba,
– Gwanda,
– Kankana
– Zuma,
– Madarar ruwa.

A kan hada su waje guda, a markada su, har sai sun zama ruwa,sai a dan kara zuma da madara. Bayan wannan,mace za ta rika sha a koda yaushe. Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe, ki hada da ganyen Alayahu, ki zuba Tumatiri da Albasa, ki yi kwadonsu, ki rika ci.

Haka nan za ki rika yin wadannan kayan lambun da ki ka markada, sai ki rika sha misali da asuba ko da sassafe kafin ki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button