
Yaron da yake kuka yana aikin birkilanci domin ya taimakawa mahaifiyarsa an bashi kyautar makudan kudade
Yaron da yake kuka yana aikin birkilanci domin ya taimakawa mahaifiyarsa an bashi kyautar makudan kudade
Kamorudeen Yaron nan mai aikin birkilanci yana sharbar kuka ya samu sha tara ta arziki bayan bayyanar bidiyon sa.
Bidiyon yaron wanda yake kuka yana aikin birkilanci ya sosa zuciyar mutane da dama, wadanda suka tausayawa yaron bisa halin da yake ciki.
Karamin yaron wanda maraya ne yana aikin na birkilanci ne domin ya taimaki mahaifiyar sa wacce take rayuwa a can wani kauye nesa da shi, kuma sau daya kawai suke haduwa a shekara.
A wani bidiyon da Lukman Shamsudeen mai amfani da “@ayom olanrewaju” a TikTok ya sake sanyawa, ya nuna ta gomashin da yaron ya samu wanda mutane suka hada masa.
Lukman ya bayyana cewa, sun sha matukar wahala kafin su gano inda mahaifiyar yaron take, domin tafiyar mai nisa ce ga kuma rashin kyawun hanya wanda hakan yasa har saida daya daga cikin motocin su ta lalace a hanya.
Ya kuma bayyana cewa, an hadawa yaron makudan kudade da suka kai N27,332,500, kamar yadda “Labarun Hausa” suka ruwaito.
Daga karshe dai sun samu sun hada yaron da mahaifiyar sa da ‘yan uwan baban sa, wadanda duk suna rayuwa ne a kauye daya.
‘Yan uwan mahaifin yaron sun amince ya cigaba da karatun sa.
Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.