Advertisement
Labaran Hausa

Yaudara: Yadda Saurayi Ya Karbi Makudan Kudi A Wajen Budurwarsa Sannan Ya Angwance Da Wata Budurwa

Yaudara: Yadda Saurayi Ya Karbi Makudan Kudi A Wajen Budurwarsa Sannan Ya Angwance Da Wata Budurwa

An gurfanar da wani mutumi ɗan kimanin shekara 30, Akeem Bello, a gaban Kotun Majistire dake Akure, babban birnin jihar Ondo bisa tuhumar ya damafari budurwarsa, Olaotan Oladapo, kudi Miliyan biyu.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa an gurfanar da Akeem ne bisa tuhuma biyu, damfara da kuma ƙarya.

Bayanai sun nuna cewa wanda ake zargin ya tafka waɗannan laifuka ne a tsakanin watan Maris zuwa Disamban wannan shekarar da muke ciki.

An ce Akeem Bello ya fara soyayya da matar da ya damafara ne tun a shekarar 2018.

Ɗan sanda mai shigar da ƙara, Insufekta A. Ajeniwa, ya faɗa wa Kotun cewa wanda ake zargin ya fara yaudarar budurwar ne a 2020 ta hanyar amfani da kuɗaɗen da take turo masa daga ƙasar waje a harkokin dake gabansa.

Insufekta Ajeniwa ya gaya wa mai shari’a cewa ana zargin Akeem ya yi amfanin da kuɗin wurin auren wata budurwa ta daban.

Ɗan sandan ya kara da cewa mahaifar wacce ke ƙara ta lalace sakamakon yawan zubar da cikin wanda ake zargi.

Yace laifin da ya aikata ya saɓa wa dokar sashi na 383 da 421,390 (b da c) dake ƙunshe a kundin dokokin manyan laifuka na jihar Ondo 2006.

Bayan sauraron ƙarar, Alkalin Kotun mai shari’a C.M Akinwumi, ya umarci a garkame wanda ake zargi a gidan gyaran halin Olokuta.

Daga nan kuma ya ɗage shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba, 2022 domin ci gaba da sauraron ƙorafin.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button